Spain – Jakadar Najeriya a kasar Sifaniya, Demola Seriki, ya riga mu gidan gaskiya.
Ɗan siyasan na Legas ya rasu ne a birnin Madrid da ke Spain, The Punch ta
rahoto.
Ya rasu yana da shekaru 63 a duniya.
An bayyana da rasuwarsa ne a ranar Alhamis kunshe cikin sanarwar mai ɗauke da sa hannun ƴaƴansa.
Sanarwar ta ce ya rasu a Madrid, Spain a safiyar ranar Alhamis.
Sanarwar ta ce:
“Tare da zukuta masu nauyi da kuma godiya ga Allah madaukakin Sarki ne muke sanar da rasuwar shugabanmu da muke kauna, miji, mahaifi, kaka, dan uwa, kawu kuma aboki.”
Takaitaccen Bayani game da mukaman da Seriki ya rike a baya
Seriki ya kasance jakadar Najeriya a Spain tun Janairun 2021.
An haifi shi ne a ranar 30 a shekarar 1959.
Kafin nadinsa a matsayin jakada, Seriki ya rike matsayi daban-daban.
Kamar yadda The Cable ta
rahoto, tsakanin 2009 zuwa Maris din 2010, shine ministan harkokin cikin gida.
Seriki ya kuma rike mukamin ministan karafa da cigaban ma’adinai daga Oktoban 2008 zuwa Disambar 2008.
Otun Aare na Legas din ya shugabanci ma’aikatar noma da albarkatun ruwa na jihar Legas daga 2007 zuwa 2008.