Jihar Zamfara – Rundunar yan sandan Najeriya a jihar Zamfara ta ce jami’anta sun ceto wasu mutane 15 da aka sace a jihar.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Alhamis, Mohammed Shehu, kakakin yan sandan jihar Zamfara, ya ce an sace mutanen ne yayin harin da yan bindiga suka kai kan hanyar Yankari-Tsafe-Gusau a ranar 1 ga watan Janairu.
Wadanda masu garkuwan suka sace sun hada da maza shida, mata bakwai da yara biyu, The Cable ta rahoto.
Sanarwar ta ce:
“Idan za a iya tunawa a ranar 1 ga watan Janairun, 2023, akwai rahoton sace wasu matafiya a hanyar Tsafe-Gusau, bayan hakan an tura jami’an yan sanda su bi sahunsu su ceto su kuma an yi nasara.
“A yayin musu tambayoyi, wadanda aka sace din sun sanar da yan sanda cewa yan bindiga masu yawa suka tare su kan hanyar Yankara-Tsafe-Gusau kusa da kauyen Magazu yayin dawowa daga Abuja da Kaduna suna hanyar zuwa Gusau, Sokoto, da Birnin Kebbi.
KU KARANTA:Â Yan Sanda Sun Kama Wata Mata Kan Yunkurin Kashe Danta A Abuja
“An tafi da wadanda aka ceto din asibitin yan sanda sannan aka musu tambayoyi kafin daga bisani aka sada su da yan uwansu da iyalansu.
“Kwamishinan yan sanda, CP Kolo Yusuf, psc, ta taya wadanda aka sace kan samun yancinsu, kuma ya ce yan sandan za su cigaba da aiki don kokarin ceto sauran mutanen.”
Tushe: News Brief Hausa