Wednesday, March 1, 2023

Yan Sanda Sun Kama Wata Mata Kan Yunkurin Kashe Danta A Abuja

Manyan Labarai

Abuja – Yan sanda a birnin tarayya a Abuja sun kama wata Comfort Alaba, mai zaune a Piwoyi a Airport Road kan zargin kashe danta dan shekara daya, The Punch ta rahoto.

Wakilin majiyar News Brief ta tattaro cewa an yi yunkurin kashe dan ne a ranar Litinin, 2 ga watan Janairu, amma wani makwabci ya ceci yaron ya kuma kira yan sanda.

Yan sandan Najeriya
Dakarun Yan Sandan Najeriya. Hoto: The Punch

Majiya ta ce:

“Ba domin makwabcin, Musbau Azeez ba da matar da kashe dan kafin daga baya wani mutumin kirki Oluwaseyi Akingbenro ya kira yan sanda.”

Akingbero ya tuntubi yan sanda da ke Lugbe a Abuja misalin karfe 10.30 na dare ya sanar da su cewa Comfort ta yi kokarin kashe danta, Michael, bayan ta buga shi a kasa amma Azeez ya ceto shi.

KU KARANTA: Kotu ta yankewa matashi daurin shekaru 235 kan laifin damfara

Daga baya an mika wacce ake zargin da wanda abin ya faru da shi hannun yan sanda wadanda suka gano wukar kicen a wurin da abin ya faru.

Abin da yan sanda suka ce kan lamarin

Da aka tuntube ta kan batun, mai magana da yawun yan sandan Abuja, Josephine Adeh, ta ce yan sandan na bincike kan lamarin.

Adeh ta ce:

“Muna bincike kan lamarin, kuma daga bisani za mu sanar da abin da bincike ya nuna.”

Tushe: News Brief Hausa

Duba nan: