Monday, November 11, 2024

Shugaban Jam’iyyar NNPP a Jihar Kaduna Ya Yi Murabus, Ya Sauya Sheka

Manyan Labarai

Shugaban New Nigeria Peoples Party, (NNPP), Ben Kure ya fice daga jam’iyyar bisa zargin wuce gona da iri da shiga sharo ba shanu na É—an takarar gwamna, Sanata Suleiman Hunkuyi, ke yi a cikin gida.

Jaridar Punch ta rahoto cewa Mista Kure yace ya tattara kayansa ya bar jam’iyyar ne saboda, “Ba zai yuwu a samu kyaftin biyu a cikin jirgi É—aya ba.”

A cewarsa, ya miÆ™a takardar yin murabus daga muÆ™aminsa ga babbar Sakatariyar NNPP ta Æ™asa tun ranar 6 ga watan Disamba, 2022 bisa zargin Hunkuyi ya hana shi aikin Ofis É—insa don É—aga kimar jam’iyya.

A ‘yan kwanakin nan tsohon shugaban jam’iyyar ba su ga maciji da É—an takarar gwamnan Kaduna a inuwar NNPP da wasu daga cikin manyan jami’an jam’iyya a jihar.

Amma da yake hira da manema labarai ranar Alhamis, 15 ga watan Disamba, 2022 a Kaduna ya bayyana cewa ya yi nadamar zama shugaban jam’iyya a jihar.

Yace: “Bana fatan ko nan gaba wani abu ya sake haÉ—a mu da shugabannin jiha.”

Saboda haka ina mai sanar da ku da kuma É—aukacin masoya na da abokanai na cewa na yi murabus daga muÆ™amin shugaban jam’iyyar NNPP reshen jihar Kaduna kuma daga yau na raba gari da jam’iyyar baki É—aya.”

Zan É—an sha iska na sarara tukunna na yi nazari kan abinda zan tunkara nan gaba da a siyasance daga bisani zan sanarwa al’umma inda da dosa.”

“Ina son faÉ—a muku cewa na aika wasikar murabus É—ina zuwa babbar Sakatariya ta Æ™asa tun ranar 5 ga watan Disamba, 2022 amma suka rarrashe ni na jinkirta su shawo kan sabanin da aka samu.”

“Suka gayyace mu muka je aka zauna kuma a makon da ya gabata Sakatariyar Æ™asa ta umarci mu shirya gangamin kamfe da tattakin nuna goyon baya a Kaduna karkashin jagoranci na amma Hunkuyi da sauran yan koransu suka shure umarnin uwar jam’iyya.”

Yayin da aka tuntuÉ“e shi domin jin ta bakinsa kan zargin wuce gona da iri da kokarin kwace iko da jam’iyya wanda tsohon shugaba ya É—ora masa, Hunkuyi ya maida martani a takaice da cewa, “Ba zan ce komai ba.”

Tushe: News Brief Hausa

Duba nan: