Monday, November 11, 2024

Nan Ba Da Jimawa Ba Zamu Shawo Kan Rikicin da Muke Fama da Shi a PDP, Gwamna

Manyan Labarai

Gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwai ya ba da tabbacin cewa jam’iyyar PDP zata shawo kan rigingimun da suka hana ta zaman lafiya a matakin ƙasa nan ba da jimawa ba.

Gwamnan ya bayyana wannan tabbacin ne yayin da yake jawabi a wurin taron masu ruwa da tsakin PDP reshen jihar Benuwai, wanda ya gudana a gidan gwamnatinsa da ke Makurdi ranar Litinin

Ortom ya amince da cewa akwai batutuwa da dama ta suka haddasa rarrabuwar kai a jam’iyyar PDP kuma a cewarsa har yanzun jagororin jam’iyya, “Na ci gaba da zaman tattaunawar neman maslaha kuma da ikon Allah zasu warware komai.”

Kan mu a haɗe yake a jihar Benuwai – Ortom

Haka zalika da yake tabbatar da cewa kan PDP a haɗe yake a matakin jiharsa, Ortom ya ce:

“Bamu da wata matsala a nan kuma kowa ya san mun shirya tsaf domin tabbatar da samun nasara a babban zaben 2023 mai zuwa.”

Gwamnan ya kara da bayanin cewa an shirya taron masu ruwa da tsakin ne domin kara dunkule wa wuri ɗaya da nazari da kara shiri gabanin zuwan 2023 domin tabbatar da ‘yan takarar PDP sun samu nasara.

Ya ce ɗan takarar gwamna a inuwar PDP kuma kakakin majalisar dokokin jihar Benuwai, Mista Titus Uba, wanda ya ɗan kwanta rashin lafiya ‘yan makonnin da suka shige ya fara murmure wa a wani Asibitin ƙasar waje, ya ba da tabbacin zasu tarbe shi a farkon makon watan Janairu, 2023.

A ruwayar Vanguard, Gwamnan ya kara da cewa:

“Kakakin majalisar wanda shi ne ɗan takarar mu na gwamna yana lafiya kalau kuma da karfinsa. Ya so ya dawo gida kafin bukukuwan Kirsimeti amma na ba shi shawarin ya jinkirta ya kara murmurewa kafin dawowa kasar nan saboda mun rike masa nan muna dakonsa.”

“Nan da makon farko na watan Janairu, baki ɗayanmu zamu tafi kofar Makurdi mu masa maraba yayin da yake dawowa gida.”

A wani labarin kuma Kotu Ta Tura Tsohon Hadimin Jonathan Gidan Kurkuku bisa cinye kuɗin makamai

Alkalin babbar Kotun tarayya, shari’a Ijeoma Ojukwu tace ta kama daraktan yakin neman zaɓen Peter Obi, Doyin Okupe da hannu a tuhumomi 26 cikin 56 da EFCC ta gurfanar da shi a kansu.

Bayan karanto masa laifukansa Alkalin ta yanke masa hukuncin zaman gidan gyaran hali na shekaru 2 ko tarar N500,000 kan kowace tuhuma ɗaya.

Duba nan: