Matar gwamnan jihar Ekiti na jam’iyyar APC mai mulkin kasar nan ta gwangwaje sabon jaririn da ya soma shigowa duniya a shekarar 2023 da sha tara da arziki.
Uwar gidan gwamnan jihar Ekiti, Dakta Olayemi Abiodun Oyebanji, ta gabatar da kyautar tsabar kuÉ—i da wasu kyaututtuka ga jaririn farko da aka haifa a 2023.
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa jaririn ya fito ne daga gidan Mista da Misis Gbenga Adeyemo a Ise Ekiti.
Jaririn na farko ya faÉ—o duniya ne da misalin karfe 12:00 na farkon ranar 1 ga watan Janairu, 2023 a Comprehensive Health Centre da ke Oke-Yadi, a Ise-Ekiti.
Jaririyar mace an haife ta da nauyin kilo 3. Uwar gidan gwamnan ta taya iyalan murnar samun karuwa kana ta bukaci su kula da jaririyar yadda ya dace.
Mahaifin yarinyar mai sana’ar aikin birkila ya ce jaririyar wacce ta zama ta biyu da suka haifa, an haife ta cikin kwanciyar hankali ba tare da wata matsala ba.
Haka nan, Mista Yetunde Salami, shugabar Asibitin ta bayyana cewa uwar da jaririyar na cikin koshin lafiya.
Bayan haka uwar gidan gwamnan na jam’iyyar APC ta kuma zarce ta kai ziyara babban Asibitin koyarwa na jihar Ekitti dake Ado-Ekiti, babban birnin jihar, inda ta ba da kyautar kudi da kayayyaki ga Mista da Misis Tons Owoeye, waÉ—an da Allah ya azurta da ‘yan uku a makon da ya gabata.
A wani labarin kuma Mahaifi Ya Lakada Wa Diyarsa Dukan Tsiya Har Lahira Saboda Ta Kira Saurayi da Wayarsa
Hukumar yan sandan jihar Akwa Ibom ta damke wani magidanci, Akaninyene Okokon, bisa zargin lakaɗa wa diyarsa ‘yar shekara 16 na jaki har rai ya yi halinsa.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Olatoye Durosinmi, yace jami’ain Hedkwatar yan sandan Ebo sun garzaya sun kama wanda ake zargi bayan samun sahihan bayanan sirri.