Thursday, May 30, 2024

Dan Najeriya ya kera motar G-Wagon, ya karade gari da abunsa a bidiyo

Manyan Labarai

Wani matashi dan Najeriya da ya kera motar G-Wagon ya sha ruwan yabo da jinjina daga wajen jama’a bayan sun ci karo da bidiyonsa a TikTok.

Kingsley Reigns Idoko, wani mai amfani da TikTok ne ya wallafa bidiyon a ranar Asabar, 31 ga watan Disamba kuma ya nuno matashin na ba motar wuta a cikin gari.

Matashin yaron ya karade cikin harabar gidansu da motar G-Wagon din inda ahlinsa suka ta jinjina masa a kan wannan hazikanci da ya nuna a bangaren fasaha.

Motar na dauke da bakin fenti kuma sak kirar G-Wagon ce da ita kuma tana yawonta ba tare da matsala ba.

Kingsley ya ce yaron kaninsa ne amma har yanzu bai yi bayanin ya aka yi ya kera motar ba.

Ya yi wa bidiyon take da: “Kanina ya kera motar G-Wagon ku tayani yada shi.”

Masu amfani da TikTok sun yaba ma kokarin yaron inda wasu da dama suka jinjinawa kokari da hazakar da yaron ya nuna a bangaren fasaha.

Kalli bidiyon nan

Jama’a sun yi martani

@user7007593736174Episode: “Mugun ido ba zai taba ganinka Amin…Allah ya kara daukaka dan uwa.”

@gilberttimothy301: “Abu ya yi kyau! Allah ya kara daukaka dan uwa.”

@Anthony moris: “Gobenka akwai haske sosai.”

@Sammy: “Abu ya yi kyau! Amma dan Allah jire logon Toyotan nan sannan ka saka naka logon.”

@user37531645809204: “Ina son sanin gayen nan.”

@Maskman: “Ya nemi nashi logon mai kyau da kansa, amfani da logon Benz kamar sadaukar da nasarar shi gare su ne.”

Mahaifi Ya Lakada Wa Diyarsa Dukan Tsiya Har Lahira Saboda Ta Kira Saurayi da Wayarsa

A gefe guda, hukumar yan sandan jihar Akwa Ibom ta damke wani magidanci, Akaninyene Okokon, bisa zargin lakaɗa wa diyarsa ‘yar shekara 16 na jaki har rai ya yi halinsa.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Olatoye  Durosinmi, yace jami’ain Hedkwatar yan sandan Ebo sun garzaya sun kama wanda ake zargi bayan samun sahihan bayanan sirri.

Durosinmi ya faɗi haka ne yayin da yake nuna wanda ake zargi tare da wasu 195 da dakarun ‘yan sanda suka kama da zargin aikata muggan laifuka daban-daban a harabar hedkwatar ‘yan sanda da ke Ikot Akpanabia, Uyo, babban birnin jahar Akwa Ibom.

Duba nan: