Wednesday, November 6, 2024

Gowon Dattijo ne: Tinubu ya Taya Tsohon Shugaban Kasa Murnar Cika Shekaru 90

Manyan Labarai

FCT, Abuja – Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yaba wa tsohon shugaban kasa, Janar Yakubu Gowon, tare da jinjina wa rayuwarsa da irin gudunmuwar da ya bayar ga Najeriya.

Tinubu ya bayyana hakan ne yayin da yake taya Gowon murnar cikarsa shekaru 90 a duniya.

Shugaban ya yi wannan yabo ne a cikin wata sanarwa da fadar shugaban kasa ta fitar, kuma aka wallafa a shafin X a ranar Juma’a, 18 ga watan Oktoba, 2024.

A cikin wannan sanarwa, Tinubu ya bayyana cewa Janar Gowon ya taka rawar gani a tarihin Najeriya, musamman wajen mulkin kasar da kuma taimakawa wajen ganin an samu hadin kai bayan yakin basasa.

Tinubu ya taya Gowon murnar cika shekaru 90
Tinubu tare da Gowon a wani taro | Hoto: @OfficialABAT (X)

Shugaban ya ce Gowon yana daga cikin manyan dattawan kasar da har yanzu ke taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban kasa.

Ya ce Gowon ya kasance mai ba shi shawara tun bayan hawansa kan shugabancin Najeriya, inda ya ba shi gudunmuwa mai yawa a fannoni daban-daban.

Tinubu ya kuma kara da cewa:

“Tun bayan hawa na kan shugabancin Najeriya, Gowon ya kasance yana ba ni shawarwari kan abubuwa da dama idan bukatar hakan ta taso.”

Ya bayyana cewa Janar Gowon ya kasance tare da gwamnati a lokuta masu wahala, musamman lokacin da aka samu sabani da wasu kasashen makwabta, inda Gowon ya bukaci a yi gyara domin tabbatar da kyakkyawar alaka tsakanin Najeriya da sauran kasashe, ta karkashin kungiyar ECOWAS.

A cikin sanarwar, Tinubu ya bayyana irin muhimmiyar rawar da Gowon ya taka wajen tabbatar da zaman lafiya a Najeriya, da kuma yadda ya ci gaba da kasancewa dattijo mai fadakarwa da jan hankali kan muhimmancin hadin kai da fahimtar juna tsakanin ‘yan Najeriya, musamman ma tsakanin addinai guda biyu da suka fi rinjaye a kasar.

Tinubu ya ce, “Bayan gudunmuwar da ya bayar a lokacin yana ofis, har yanzu Gowon yana cigaba da kasancewa dattijo mai martaba tare da nuna muhimmancin shekaru da addu’o’i ga ci gaban kasar.”

Haka zalika, Tinubu ya yaba wa Gowon bisa irin rawar da yake takawa wajen wanzar da zaman lafiya da hada kan ‘yan kasa.

Ya jaddada cewa Gowon ba wai kawai dattijo bane, amma kuma yana koyar da zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin mabiya addinai daban-daban.

Shugaban kasar ya bayyana cewa irin jagoranci da dattako da Gowon ke nunawa ya kasance abin koyi ga matasa da sauran shugabannin kasa.

A cewar Tinubu, Janar Gowon ya nuna jajircewa da kishin kasa a lokacin mulkinsa da bayan barinsa ofis, kuma yana ci gaba da kasancewa daya daga cikin dattawan da ke bayar da muhimmiyar gudunmowa ga al’ummar Najeriya da duniya baki daya.

Tinubu ya kammala da taya Gowon murna tare da addu’ar Allah ya kara masa lafiya da tsawon rai, domin ci gaba da gudanar da ayyukan alheri da ake damawa da su.

 

Duba nan: