A kullun ana kara samun ci gaba a duniya duba ga yadda ake kirkiran abubuwan ban mamaki da daukar hankali.
A halin da ake ciki a yanzu, kasar Jamus ta kirkiri wani inji na kyankyasar jarirai tare da rainonsu kamar a mahaifar uwa.
Injin kyankyasar wanda ake yiwa lakabi da ‘Ecto Life’ zai samar da dukkanin abubuwan da ‘da yake bukata a cikin mahaifar uwarsa harma da wasu kari.
Wannan inji ya girgiza duniya sosai domin dai shine irinsa na farko da aka fara samarwa kamar yadda rahotanni suka nuna.
Kwararrun likitoci da masana sun shafe shekaru 50 suna kokarin samar da injin
Kamar yadda rahotanni suka nuna, an shafe fiye da shekaru 50 ana kera wannan na’urar, wanda manyan likitoci da masana suka bayar da gudunmawa wajen ganin ya tabbata.
An kuma rahoto cewa injin zai iya kyankyashe jarirai 30,000 a cikin shekara daya.
Hashem Al-Ghaili, wanda shine ya kirkiri injin ya bayyana cewa na’urar zai taimaka sosai wajen kawo karshen matsalolin da mata ke fuskata yayin goyon ciki da haihuwa.
Har ila yau, Ecto Life zai taimakawa matan da likitoci suka ce ba za su iya haihuwa ba da wadanda aka cire mahaifarsu saboda cutar daji, da kuma kawo karshen mutuwa da mata ke yi wajen haihuwa.
Injin zai taimaka wa kasashen da yawansu ke raguwa kamar su Japan da Bulgeria da kuma Koriya Ta Kudu ta hanyar kyankyashe masu yara masu yawa.
Iyaye za su zabi hallitar dansu da kuma yaren da suke so ya ji
Wani babban abun al’ajabi kuma, mutum zai koyawa jinjiri irin yaren da yake so ya koya sannan zai saka masa irin kaifin basirar da yake so.
Har ila yau, mutum zai zabi irin launin fatan da yake so jinjirin ya kasance da shi da kuma kalar kwayar idonsa, gashi da yanayin hallitar yaron gaba daya.
Injin Ecto Life zai kuma ba jarirai kariya daga kamuwa da cututtukar da yara kan kamu da shi a lokacin da suke cikin cikin iyayensu.
Sai dai babu tabbaci kan ko zai samu karbuwa a wajen jama’a musamman a bangaren masu ra’ayin riko da koyawar addini.
Tushe: News Brief Hausa