FCT, Abuja – Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya daow Najeriya bayan shafe kwanaki yana hutu a kasashen ketare.
Rahotanni sun tabbatar da cewa jirgin da ke dauke da shugaban ya iso ne a yammacin Asabar, amma ba a sami damar ganin shugaban kai tsaye ba a lokacin da ya sauka.
Shugaba Bola Tinubu ya sauka a filin jirgin saman Abuja, inda Olusegun Dada, mai taimaka masa wajen kafofin sadarwa na zamani, ya tabbatar da saukar jirgin fadar shugaban kasar a shafinsa na X.
Dada ya wallafa hoton saukar jirgin tare da rubuta sakon maraba da dawowar shugaban kasa, yana cewa, “Barka da zuwa shugaban kasa.”
An tabbatar da isowar Tinubu Najeriya kimanin karfe 7:20 na yammacin ranar Asabar, 19 ga Oktoba, kamar yadda aka bayyana a dandalin sada zumunta.
Wasu bidiyo guda biyu da aka wallafa sun nuna jirgin shugaban kasar yana sauka a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe na Abuja.
A cikin wani gajeren bidiyo, an ga wasu mutane suna fareti a cikin duhu, suna tarbar shugaban kasa, kamar yadda aka saba a irin wannan yanayi.
Shugaba Tinubu ya kammala hutunsa a Turai, inda ya shafe makonni biyu yana hutawa a Birtaniya.
Rahoton The Cable ya tabbatar da cewa Tinubu ya kwashe kwanaki 17 a kasashen Ingila da Faransa kafin ya dawo gida.
Idan za a iya tunawa, Tinubu ya bar Najeriya ne a farkon watan Oktoba, domin samun lokaci na hutu bayan gudanar da ayyukan mulki.
Ana sa ran cewa shugaban kasa zai koma ofis ranar Litinin mai zuwa, inda ake tsammanin zai jagoranci zaman majalisar zartarwa ta kasa (FEC).
Haka kuma, ana ta rade-radin cewa tafiyar da Tinubu ya yi zuwa ketare na iya zama wata dama gareshi domin yin canje-canje a cikin majalisar ministocinsa, yayin da ake cigaba da nazarin ayyukan gwamnati.