Wata caudediyar budurwa da ta shafe shekaru 15 tana rayuwa a birnin Dubai tare da uwar gidanta ta waiwayi gida Najeriya.
Budurwar ta garzaya shafin sada zumunta watau TikTok, inda ta sanar da batun dawowarta gida Najeriya da wani bidiyon lokacin da ta sauka a filin sauka da tashin jiragen sama.
Matar wacce ta bayyana cewa ta dawo gida ziƙau watau hannu rabbana tace Allah ya sa ta dawo cikin ƙoshin lafiya.
Sai dai matar wacce ta taso daga hadaddiyar daular larabawa zuwa gida Najeriya ta ayyana babban burinta na samun wanda zai yi wuff da ita su shiga daga ciki.
Wannan bidiyo da ta wallafa ya yi yawo a dandalin TikTok kuma ya haddasa cece-kuce inda mutane suka bayyana ra’ayoyin su mabanbanta.
Wasu daga ciki sun mata fatan Alheri a neman mashinshini. News Brief Hausa ta É—auko musu wasu daga cikin martanin jama’a a soshiyal midiya.
amejumatimeyin ya ce:
“Yar uwa ba bu miji a Najeriya shawara ta ki koma inda kika hito Dubai in ba so kike ki yi biyu ba bu ko É—aya ba”
Wani mai suna User74 ya rubuta cewa:
“Kar ki cire rai muna da mutanen kirki a Najeriya kuma zaki iya haÉ—auwa da É—aya.”
Simom Ezoba ya ce:
“Shekara 15 ba kaÉ—an ba gaskiyar uwar dakinki ta kai zuciya nesa, ina miki fatan alheri a neman mijin da kika sa a gaba.”
Brooklyn ya ce:
“Ni abun da ya shige mun duhu nake son sani shi ne meyasa kika zauna tsawon wannan lokacin amma baki tara ko sisi ba.”
A wani labarin kuma Budurwa ta ari na kare yayin da soja ya fatattaketa bayan ta zolaye shi a bidiyo
Wata budurwa ta yi gudun neman tsira bayan ta zolayi wani Sojan Najeriya da ke zaune yana hutawa a kasan wata bishiya.
A bidiyon da ta wallafa a soshiyal midiya, budurwa ta je wurin ta mika wa sojan wata takarda mai É—auke da rubutun ‘KAI BABBAN HAMAGO NE’ sai dai lamarin bai kare ta dadi ba.