Thursday, August 31, 2023

Budurwa ta ari na kare yayin da soja ya fatattaketa bayan ta zolaye shi a bidiyo

Manyan Labarai

Wata ‘yar Najeriya ta gudu don tsira da ranta bayan ta yi wa wani soja wani mugun wasa.

A wani bidiyo da ya yafu a TikTok, an gano lokacin da budurwar ta isa gaban sojan sannan ta yi saurin arcewa bayan ta mika masa wata takarda dauke da rubutun ‘KAI KATON WAWA NE’.

Ba tare da bata lokaci ba, sojan ya tashi daga inda yake zaune, ya karya wani reshen jikin bishiya sannan ya bi budurwar da gudu.

A lokacin da ya cimmata ne sai take bayyana masa cewa wasan tsokana ne ba wai tana nufin zaginsa da gaske bane.

An gano ta tana aikin bashi hakuri sannan ta nunawa sojan mutumin da ke rike da kamara a inda ya boye.

Kalli bidiyon anan:

Jama’a sun yi martani

Tiko ya ce:

“Ashe kin iya gudu shine kike tsokanar soja. Sojan ya tsaya ya karya bulala amma duk da haka ya cimma ki ba tare da yayi gudu ba ma.”

OLASUNKANMI ya ce:

“Allah ya so ki da kin ji a jikinki da ace mutumin bai yarda ba. Karfin kasancewa mace kenan.”

Unknown Lincoln ya ce:

“Hakan ya tuna mun da lokacin da nake nadir bidiyon wani fada sai wani yace kama mai nadir kamarar shima.”

Olushola Olatunji ta ce:

“Wannan yana daya daga cikin damar da mata ke samu a waje. Da ace na miji ne, da mutuwarsa ta zo.”

Çåll Mê Mønïtãlä Ômë ta ce:

“Amma me zai sa ki fadi irin haka idan saurayinki ne za ki iya gwada hakan a kansa Allah ya kyauta maku…”

Daniel Gstepz ya ce

“Chai… kin ci sa’a baki hadu da sojan da ya yi makaranta sannan ya san menene zolaya ba. Da jikinki ya fada maki.”

MC C10 ya ce:

“Da ace ta juya sannan ta ga cewa mai daukar kamarar baya nan.”

A wani labarin, masu amfani da soshiyal midiya sun yi martani ga wasikar soyayya da wata yarinya ta rubutawa matashi dan aji hudu a Sakandare mai suna Somto.

Yayar yaron ta wallafa wasikar a TikTok yayin da take ja masa kunne kan harkokin makarantarsa.

Ta bukaci kanin nata ya durkusa yayin da take masa tambayoyi kan siffar marubuciyar wasikar mai suna Precious.

 

 

Duba nan: