FCT, Abuja – Farfesa Emmanuel Osodeke, shugaban kungiyar malaman jami’o’in Najeriya, ASUU, ya ce gwamnatocin da suka gabata sun fi tausayawa lakcarori, LIB ta rahoto.
Da ya ke magana wurin taron kaddamar da littafan karatu 50 na makarantun gaba da sakandare da marubutan Najeriya wadanda TETFund ta dauki nauyi suka wallafa, a ranar 5 ga watan Janairu, Osodeke ya bayyana wasu abubuwa da suka faru da su karkashin gwamnatin mulkin soja.
Gwamnatin sojoji ta fi damuwa da halin da lakcarori suke ciki – Farfesa Osodeke
Ya ce:
“Na gode maka sosai mai girma minista da dukkan mu da muka taho wurin nan a yau. Ina son gode wa takwarori na saboda tada batun kuma ina ganin suna da muhimmanci. Zan dan ce wani abu game da TETFUND da yadda ta samo asali?
“A 1992, kungiyar tana yajin aiki kuma muna tattaunawa; yadda muke yi a wancan lokacin da Obafemi da wasu, kuma da muka gama, gwamnati za ta ce ta yadada zamu biya sai mu ce ku kallubale mu. Kuma suka kallubale ASUU, kasa da kwana uku muka kawo shawarar TETFUND, kuma gwamnatin ta amince, gwamnatin soja.
“Na ga cewa sojojin ma sun fi tausayi. Sai aka kafa TETFUND. An saka hannu kan dokar a 1993. Sai da ASUU ta tafi yajin aiki na uku kafin aka kafa kwamitin TETFUND kuma aka saki kudin fara aiki.”
KU KARANTA:Â Okorocha Ya Fayyace Gaskiya Kan Batun Komawarsa PDP
Da ya ke tsokaci kan tsarin ‘ba aiki ba biyan kudi’ na gwamnatin tarayya wacce yasa ba a biya lakcarori albashin wata takwas ba, Osodeke ya yi kira ga yan Najeriya su matsa wa gwamnati lamba ta ceto manyan makarantu daga rushewa.
Shugaban na ASUU ya yi kira a kara harajin ilimi daga 2.5 % zuwa 10% don TETFUND ta samu karin kudin da za ta warware matsalolin da ke adabar bangaren ilimi.
Kotu Ta Dakatar da Hukumar DSS Daga Kama Shugaban INEC
A wani rahoton, wata babbar kotun tarayya ta dakatar da karar da ke neman a tsige Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu daga mukaminsa kan zargin ba da bayanan karya a kan kadarorinsa.
Alkalin kotun, Mai Shari’a M. A. Hassan ya ki amincewa da bukatar da wasu 14 da masu karar suka gabatar a ranar Laraba, 4 ga watan Janairu, jaridar Daily Trust ta rahoto.
Tushe: News Brief Hausa