Thursday, August 31, 2023

An Kama Wani Hatsabibin Barawon Mota Da Ya Bar Kano Zuwa Bauchi Don Sata

Manyan Labarai

Jihar Bauchi – Gwamnatin Jihar Bauchi ta kama wani hatsabibin mai kwace wa mutane motoccin bayin Allah mai suna Mohammed Bashir.

Kakakin yan sanda, SP Ahmed Mohammed Wakil, cikin wata sanarwa a ranar Alhamis, 5 ga watan Janairu, ya ce jami’an hedkwatar yan sanda na ‘B’ Division ne suka kama Bashir a Mariri, Jihar Kano.

 

Suspect In Bauchi
Wanda ake zargi da satar mota a Bauchi. Hoto: LIB

A cewar mai magana da yawun yan sandan, wanda ake zargin, da abokin harkallarsa da yanzu ake nema sun taho daga Kano ne don cigaba da kwace motoccin mutane a Bauchi.

Yadda aka kama Bashir, wanda ake zargi da satar motocci a Bauchi

Sanarwar ta ce:

“A ranar 28 ga watan Disamban 2022, an samu kiran neman dauki cewa an sace wa wani motarsa Toyota Corolla a garejin kanikawa da ke hanyar Sa’adu Zungur a Bauchi.”

“Bayan kiran, DPO ya tura tawaga zuwa wasu wuraren a yankin kuma aka yi nasarar kama wanda ake zargin aka kwato motar.”

Sanarwar ta cigaba da cewa an gano makullin motocci uku da katin shaida na jami’in NSCDC da sunan wanda ake zargin a jikinta.

Wanda ake zargin ya ce ya taba yin aiki a matsayin jami’in sa kai da NSCDC kafin a kore shi a 2020. Ya kuma ce wani Hamidu a jihar Kano ne ya koya masa kwace motocci.

Kwamishinan yan sanda, CP Aminu Alhassan ya umurci jami’ansa su kara sa ido don ganin an kamo dayan wanda ake zargin da nufin kwato sauran motoccin satan.

Yan Sanda Sun Ceto Matafiya 15 Da Aka Sace A Zamfara

A wani rahoton, rundunar yan sandan Najeriya a jihar Zamfara ta ce jami’anta sun ceto wasu mutane 15 da aka sace a jihar.

A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Alhamis, Mohammed Shehu, kakakin yan sandan jihar Zamfara, ya ce an sace mutanen ne yayin harin da yan bindiga suka kai kan hanyar Yankari-Tsafe-Gusau a ranar 1 ga watan Janairu.

Wadanda masu garkuwan suka sace sun hada da maza shida, mata bakwai da yara biyu, kamar yadda Jaridar The Cable ta rahoto.

Tushe: News Brief Hausa

Duba nan: