Jihar Imo – Tsohon gwamnan jihar Imo kuma sanata mai wakiltar Imo West, Owelle Rochas Okorocha ya karya ikirarin cewa ya shiga jam’iyyar PDP, rahoton LIB.
Rahotannin cewa dan majalisar ya shiga jam’iyyar hamayyar ne bayan an gan shi a wani hoto tare da tsohon gwamna Emeka Ihedioha a wurin jana’izar daya cikin hadimansa, Pascal Uju.
Amma, cikin wani sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis 5 ga watan Janairu, Okorocha ya ce har yanzu shi dan jam’iyyar APC ne.
Rochas ya karyata cewa ya shiga PDP
Sanarwar mashawarcinsa na musamman kan kafafen watsa labarai, Sam Onwuemeodo ya fitar ta ce:
“Masu daukan hotuna suna aikinsu ba tare da sanin cewa wasu mutane na da mugun nufi ba, tunda dukkan shugabannin siyasa sun halarci wurin don jana’izar mahaifiyar Hon. Uju. Ba taron siyasa bane.
“Wadanda suka yada wannan labarin karyar ba su ambaci inda aka dauki hoton da dalilin zuwa wurin ba.
KU KARANTA:Â APC: Kotun Daukaka Kara Ta Ba Uba Sani Nasara, Ta Yi Fatali Da Karar Sha’aban
“Ba su iya ruwaito wani abu cikin jawabin Okorocha ba tunda shi ba bebe bane don haka dole ya yi jawabi a wurin.
“Hankalin mu kwance za mu iya cewa Okorocha bai shiga PDP ba.
“Har yanzu shi dan APC ne. Babu yadda za a yi jana’iza ta zama taron siyasa.”
Tushe: News Brief Hausa