Thursday, November 7, 2024

Na Dena Jin Dadin Rayuwa, Fata Na Kawai Shine Cikawa Da Imani, Attajirin Dan Kasuwa Aminu Alhassan Dantata

Manyan Labarai

Kano, Kano – Dattijon kasa, kuma fitaccen dan kasuwa, Aminu Alhassan Dantata, ya bayyana cewa ya dena jin dadin rayuwa kuma yana fatan zai bar wannan duniyan cikin imani.

Dantata, mai shekara 91, ya bayyana hakan ne yayin da ya tarbi mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar APC, Sanata Kashim Shettima, Daily Trust ta rahoto.

 

Aminu Dantata
Aminu Alhassan Dantata. Hoto: Triumph News

Ya bayyana cewa tun da kuriciyarsa, ya samu damar haduwa da mutane da dama da kulla abota a dukkan jihohin Najeriya amma a yanzu da wuya zai iya tuna 10 cikinsu da ke raye.

Na gaji da rayuwa, galibin wadanda na sani sun rasu, ina fatan in mutu cikin imani – Dantata

Kalamansa:

“Na ziyarci dukkan jihohin Najeriya kuma na yi harkoki da mutane a jihohin, da damansu abokai na, amma abin bakin ciki, dukkan mutanen da na sani, da wuya zan iya kiran sunan 10 da ke raye.

“A gaskiya, yanzu, ina jiran lokaci na ne kawai. Bana jin dadin rayuwa kuma. Ina fatan zan bar duniya da imani.

“Ina fatan ban yi wa wani laifi ba a rayuwa. Idan na yi wa wani laifi, ina fatan su yafe min. Idan wani ya min laifi, na yafe musu.

“Ni ne kadai a yan uwanmu na rage na ke rayuwa da jikoki.”

Dantata ya yi wa Najeriya addu’a

Dantata, yayin bayyana murna da jin dadi bisa ziyarar, ya yi addu’a ga Najeriya ta samu zaman lafiya da lumana.

“Kada Allah ya kyale mu da iyawan mu, muna addu’a Allah ya cigaba da kare mu da kiyayye mu,” ya kara da cewa.

KU KARANTA: Yara 102: A Karshe, Manomi Mai Jikoki 568 Ya Yanke Shawarar Daina Haifan Yara

Shettima ya ziyarci cibiyar kansa da ake ginawa a Kano

Tunda farko, Shettima, wanda ya ziyarci jihar don tuntuba, ya bayyana cewa ya ziyarci dattijon ne kan ayyukan da ake yi a arewa gabanin babban zaben 2023.

Ya kai ziyarar ne tare da gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje, Musa Gwadabe, Janar Lawal Jafaru Isah da Tanko Yakasai.

Ya kuma ziyarci cibiyar Kansa wanda ake daf da kammalawa kafin ya tafi filin tashin jiragen sama.

Tushe: News Brief Hausa

Duba nan: