Thursday, August 31, 2023

Zan Kwaci Kujerar Sanata a Zaben 2023 Da Karfin Tsiya, Gwamnan APC

Manyan Labarai

Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, ya ce zai kwaci kujerar Sanata mai wakiltar mazabar Ebonyi ta kudu a babban zaɓen 2023 mai zuwa.

Jaridar Punch ta tattaro gwamna Umahi na bayyana cewa zai tafi majalisar tarayya ya yi fafuka domin mutanen jihar Ebonyi.

A cewar wata sanarwa da mai taimaka wa gwamna Umahi na musamman kan harkokin midiya da dabaru, Chooks Okoh, ya fitar, gwamnan ya yi wannan furucin ne a mahaifarsa Uhuru da ke karamar hukumar Ohaozara ranar Laraba, 28 ga watan Disamba, 2022.

Da yake jawabi ga dandazon magoya baya a wurin gangamin taron da aka shirya dominsa, gwamna Umahi ya ce:

“Zan tafi asalin cibiya na yi yaki domin samun walwala da jin daɗin al’ummar jihar Ebonyi, rage zaman kashe wando da muhimman ayyuka kasa.”

“Zan yi yaƙi domin a tallafawa mazauna jihar Ebonyi. Zamu kwaci kujerar nan ko da tsiya ne.”

Sanarwar ta kara ɗauko kalaman Umahi yayin da yake cewa yana da kwarewa da gogewar da ake bukata na wakiltar mutane ba wai na Ebonyi ta kudu kaɗai ba, jihar baki ɗayanta da kabilar ibo kafataninta.

Daga nan kuma ya tabbatar wa da mazauna mazaɓarsa cewa zasu ji daɗi idan suka tura shi wakilci kuma zai tafi da kowa babu nuna banbanci ba da alfahari.

Bugu da kari, gwamna Umahi ya caji mazauna shiyyar Ebonyi ta kudu da su goyi bayan ɗan takarar gwamnan jihar a inuwar APC, Francis Nwifuru, a babban zaben 2023 mai zuwa.

A wani labarin kuma A Watan Janairu Zan Sanar da Ɗan Takarar Shugaban Kasan Da Zan Goyi Baya a 2023 inji gwamna Wike

Gwamnan jihar Ribas, wanda ya raba gari da dan takarar shugaban kasa a inuwar jam’iyyarsa ta PDP, yave jira ya kare kowa na gab da sanin dan takarar da xai tallata gabanin 2023.

Wike, jagoran tawagar gaskiya watau G-5 yace a watan Janairu na shekar mai kamawa zai bayyana wa duniya wanda ya dauka.

Duba nan: