Thursday, August 31, 2023

Zaben 2023: Dan Takarar Majalisar PDP Ya Rasu A Abuja

Manyan Labarai

Barista Abba Bello Haliru, dan takarar Majalisar Tarayya a Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a mazabar Birnin Kebbi/Kalgo/Bunza, ya rasu.

Da yake tabbatar da mutuwarsa, darakta janar na kwamitin yakin neman zaben PDP, Alhaji Abubakar Shehu, ya ce marigayin ya rasu ne bayan yar gajeruwar rashin lafiya a ranar Juma’a, Daily Trust ta rahoto.

Bello ya rasu ne bayan dawowa daga ziyartar mahaifinsa, Muhammed Haliru Bello wanda tsohon shugaban jam’iyyar PDP ne a Kebbi, da ke jinya a Amurka.

Dan takarar na PDP, ya lashe zaben fidda gwanin jam’iyyar da aka gudanar a watan Mayu.

Bello ya kayar da dan majalisar da ke ci a yanzu, Alhaji Mohammed Bello Yakubu wanda hakan ya sa ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC.

An tsayar da harkokin kamfen

Kwamitin yakin neman zaben ya kuma yi umurnin tsayar da duk wasu harkokin kamfen har zuwa wani lokaci nan gaba.

Ciyaman din kwamitin watsa labarai, Alhaji Lawal Gwandu, ta yi kira ga shugabannin PDP da mambobin jihar da magoya baya su yi addu’a Allah ya jikan mammacin.

Kwamitin kamfen din gwamna na jihar ta kuma mika sakon ta’aziyya ga iyalan, masarautar Gwandu da daukacin mambobin jam’iyyar PDP baki daya bisa wannan babban rashi da suka yi.

Okorocha Ya Fayyace Gaskiya Kan Batun Komawarsa PDP

A wani labari na daban, tsohon gwamnan jihar Imo kuma sanata mai wakiltar Imo West, Owelle Rochas Okorocha ya karya ikirarin cewa ya shiga jam’iyyar PDP.

Rahotannin cewa dan majalisar ya shiga jam’iyyar hamayyar ne bayan an gan shi a wani hoto tare da tsohon gwamna Emeka Ihedioha a wurin jana’izar daya cikin hadimansa, Pascal Uju.

 

Duba nan: