Thursday, May 30, 2024

Za A Rataye Wani Soja Har Sai Ya Mutu A Borno Saboda Kashe Abokin Aikinsa Da Wasu Mutane 5

Manyan Labarai

Borno – Kotun soji ta samu Musa Saleh da laifin kashe abokin aikinsa da wasu mutane biyar da ba su ji ba ba su gani ba, lamarin da ya haddasa musu raunuka da nakasa ta dindindin, rahoton LIB.

An yanke wa wani soja mai suna Private Musa Saleh hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda kashe abokin aikin sa a garin Mafa da ke jihar Borno. Babban Kotun Sojan Najeriya ta 7 ta Sojoji ta same shi da laifin kuma ta yanke hukuncin.

An yanke wa wani soja hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda halaka abokin aikinsa

An tuhumai Musa Saleh kan laifuka 4 da suka hada da kisan kai, kai hari, da kuma yunkurin kisa. Ya de musanta aikata laifukan.

Kotun sojin karkashin jagorancin Brig. Gen. Richard Pam, ya samu sojan (wanda ke 112 Task Force Battalion a Mafa) da laifukan da ake tuhumarsa da shi sannan kuma ya gano cewa ya kashe mutane 5 da ba su ji ba ba su gani ba, ya yi sanadin jikkata wasu kuma ya bar wasu kuma da nakasa ta dindindin.

Mai gabatar da kara ya gabatar da shaidu 6 da kuma abubuwan shaida 11 don tabbatar da tuhume-tuhumen. Mai kare wanda ake tuhuma kuma ya gabatar da sojan da ake tuhuma a matsayin shaida shi kadai.

Brig.-Gen. Pam ya ce bayan ya duba shaidun da aka gabatar wa kotun soji, ya bayyana a fili cewa an keta dokokin.

Ya ce:

 

“Kotun Sojin ta yanke hukuncin daurin rai-da-rai ga Musa Saleh kamar haka: Kisa ta hanyar rataya , daurin watanni 24 a gidan yari, da kuma daurin rai da rai.”

Ku Karanta: Rudani A Kotu Yayin Da Wani Mutum Ya Yi Kokarin Nuna Wa Alkali Mazakutansa

Lauyan da ke kare mai laifi Habib Kabura Batuncha ya zanta da manema labarai inda ya ce:

An kawo karshen shari’ar da ake yi tsakanin Sojojin Najeriya da Musa Saleh kuma za su yi abin da ya dace a lokacin da ya dace.

Tushe: News Brief Hausa

Duba nan: