Thursday, May 30, 2024

Yanzu-Yanzu: Gobara ta Kama a Hedkwatar Tsaron Najeriya

Manyan Labarai

FCT, Abuja – An yi gobara a hedkwatar tsaro na Najeriya da ke birnin tarayya Abuja a ranar Litinin, rahoton The Punch.

Gobarar, wanda kawo yanzu ba a san sanadin ta ya, ya faru ne a bene na biyu a ginin na DHQ. An tattaro cewa jami’an hukumar kwana-kwana na tarayya da jami’an sojoji suna kokarin kashe wutar.

 

Hedkwatar tsaro ta tabbatar da afkuwar gobarar

Direkta na sashin watsa labarai na DHQ, Manjo Janar Jimmy Akpor, ya tabbatar da lamarin.

Ya kara da cewa an samu nasarar cin galaba kan gobarar, ya kuma ce an fitar da dukkan ma’aikata da ke cikin ginin.

Ya ce:

“Wani karamin gobara ya faru a bene ta biyu a hedkwatar tsaro, Garki Abuja da rana a yau 12 ga watan Disamban 2022. Ba a san abin da ya janyo gobarar ba a yanzu.

“Sai dai, abubuwa sun daidaita a yanzu. Ana bincike don gano abin da ya yi sanadin gobarar.

“Muna godiya ga hukumar kwana-kwana ta tarayya da al’umma bisa goyon baya da fatan alheri da suka yi wa dakarun sojojin Najeriya.”

Tushe: News Brief Hausa

Duba nan: