Wednesday, March 1, 2023

Yan Bindiga Sun Kashe Shugaban Jam’iyyar APC

Manyan Labarai

An barbe shugaban jam’iyyar APC na gundumar Umuchoke, karamar hukumar Onuimo ta jihar Imo, Christian Ihim, har lahira.

Wasu miyagun yan bindiga sun halaka shugaban APC na gundumar Umuchoke, ƙaramar hukumar Onuimo a jihar Imo da ke kudu maso gabashin Najeriya.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa bayan wannan É—anyen aiki, yan bindigan sun tattara mambobin jam’iyyar guda 5 sun yi awon gaba da su.

Rahotannin da suka fito yau Laraba sun nuna cewa maharan sun ci gaba da buɗe wuta ba kakkautawa tsawon daren Talata, lamarin da ya tilastawa mazauna ƙauyen guduwa neman tsira.

Baya ga kisa da garkuwa da jiga-jigan APC, yan bindigan sun zarce zuwa ƙauyen Okwelle, ƙaramar hukumar Onuimo, suka yi awon gaba da wata mambar APC hallau mai suna, Onyinyechi Egenti.

An ce marigayi shugaban jam’iyyar ya kasance tsohon hadimin Sakataren tsare-tsare na Æ™asa da ya gabata, Emma Ibediro.

“An kashe shugaban jam’iyar APC na gundumar Umuchoke, Æ™aramar hukumar Onuimo. Bayan wannan kisan maharan sun yi garkuwa da wasu mambobin jam’iyya 5 a kauyen.”

“Daga nan suka zarce zuwa kauyen Okwelle suka haÉ—a da wata mambar APC mace, Onyinyechi Egenti. Yankin mu ya zama abun tsoro, sun bude wuta kai kace muna cikin lokacin yaki ne.” inji wata majiya.

Idan baku manta ba a ranar 15 ga watan Disamba, 2022 yan bindiga suka kashe É—an takarar majalisar jiha mai wakiltar mazabar Onuimo na jam’iyyar Labour Party, Christopher Elehu, bayan sun kone Æ™auyen su Okwe.

Yan bindiga sun kashe jami’ar yan sanda

Haka zalika wasu bayanai sun nuna cewa wasu yan bindiga sun kashe jami’ar hukumar yan sanda mace.

An tattaro cewa maharan sun kai farmaki shingen ababen hawa da ke kan titin Aba-Owerri, inda ita marigayyar da sauran abokanan aikinta suka fafata da yan bindigan.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Henry Okoye ya yi alkawarin gudanar da bincike kana ya dawo gare mu amma har yanzu shiru.

A wani labarin kuma PDP Ta Dakatar da Sanata Mai Ci da Wasu Jiga-Jigai 7 Kan Abu 1

Mai magana da yawun PDP, Debo Ologunagba, shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar da daren Jumu’a,

Tushe: News Brief Hausa

Duba nan: