Thursday, August 31, 2023

Yadda za a Iya Bambamce Asalin Kudi da Jabu

Manyan Labarai

Tun bayan da babban bankin Najeriya ya fitar da sabbin takardun kudi korafe-korafe sun yi ta biyo baya game da yadda aka samu bullewar takardun bogi a cikin kudaden wanda hakan ya haifar da damuwa matuka.

Sai dai kuma a cewar babban bankin Najeriya, takardun kudin an kewaye su da matakan tsaro da kariya don saukaka yadda za a gane Mai kyau da jabu cikin sauki.

Za a iya banbace kudin ta hanyar gani da kuma tabawa wanda kalan Fenti na cikin abinda za ai saurin ganewa. Hoton,haruffa da lambobi.

Don kubutar da ‘yan Najeriya daga fadawa hannun Jabun kudi shi yasa muka shirya kawu muku wannan bayani.

Siririn layi da ya tsirga daga saman kudi zuwa kasa

Akwai wani siririn layi da tsirga daga sama zuwa kasan kudi Wannan tsiri ana samun shi ne a kowace cikin kowace takardar kudi ta gaske.

Jabun kudi ba zai taba samun wannan layin ba sai dai wanda ya yi kama dashi.

Tambarin da ke kusa da sa hannun Shugaban Babban Bankin

A ta gefen hannun dama akwai wani tambari mai kama da ruwan zinare foil kusa da sa hannun gwamnan CBN.

Mutun na iya amfani da wannan wajen gwada ingancin wannan kudi ta hanyar gwada dayewa in ya daga to wannan kudi jabu ne in kuma bai bare ba to na gasken ne.

Bincika ingancin takarda

Ana yin takardun kudi ne da takarda ta musamman, yayin da jabun kudi ana yin su ne daga takardun da aka saba gani.

Tabbatar da hakan abune mafi sauki, ka riƙe ainihin kudi yadda zaka ji su a hannun ka zakai saurin tantacewa.

Launin kudi

Launin kudin gaske ya banbanta ko a ido shi kuma jabun kudi zakagan shi da dishi dishi. In ka daga a cikin haske zakaga hotun jiki kalan a watse.

An bada tabbacin cewa a yanzu haka jabun kudi na nan na yawo wanda wani ganau ne ya tabbatar da hakan.

A wani labari na daban, babbar Kotun tarayya mai zama a Abuja ta kama tsohon mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin hulɗa da jama’a, Doyin Okupe da laifin karkatar da wasu kuɗin makamai daga Ofishin babban mai ba da shawara kan tsaro.

Alkalin Kotun mai shari’a Ijeoma Ojukwu a ranar Litinin ta yanke cewa ta kama Okupe da hannu dumu-dumu a halatta kuɗin haram kuma ta ci shi tarar naira miliyan N13m.

Duba nan: