Thursday, May 30, 2024

Yadda Kwastoma Ya Caka Wa Ƴar Gidan Magajiya Mai Shekara 55 Wuƙa Yayin Da Suke Jayayya

Manyan Labarai

Nairobi, Kenya – An caka wa wata yar gidan magajiya mai shekara 55, Savelina Anatoli, wuka yayin da rikici ya shiga tsakaninta da kwastomanta, LIB ta rahoto.

Yan sanda a yankin Shauri Moyo, a Nairobi, sun kaddamar da bincike a kan batun caka wukar a halin yanzu ya sa aka kwantar da Savelina Anatoli a asibiti.

Yan mata
Yan mata. Hoto: Nairobi News.

Kwastoman, wanda ba a san ko wanene ba, ya daba mata wuka a gefen hagu na wuyan ta kafin ya tsere zuwa wani wurin da ba a sani ba a yanzu.

Sai dai, ya kuma bar kayayyakinsa ciki har da wukar da jami’an ‘yan sandan suka dako daga wurin da lamarin ya faru.

Yan sanda sun gano wukar da aka yi amfani da ita wurin harin

Rahoton na yan sanda ya ce:

“An caka wa wata yar gidan magajiya yar shekara 55 mai suna Anatoli wuka a gefen wuyanta sakamakon jayayya da kwastomanta. Mutumin ya tsere ya bar kayansa da aka gano a wurin ciki har da wukan da ya yi amfani da shi wuka caka mata.”

An garzaya da wacce abin ya faru da ita zuwa asibitin MSF Hospital Mathare kafin daga bisani aka mayar da ita Mama Lucy Hospital inda a halin yanzu tana kwance a can.

Tushe: News Brief Hausa

Duba nan: