Saturday, June 1, 2024

Yadda Amarya Ta Shararawa Ango Mari a Wajen Daurin Aure, Sun Ba Hammata Iska

Manyan Labarai

Wata fusatacciyar amarya ta dambatu da angonta a yayin daurin aurensu inda ta shararawa masa mari mai kwance kunne a fuska.

Bidiyon ma’auratan wadanda suka ba hammata iska a ranar daurin aurensu ya samu mutum fiye da 92k da suka kalle shi a kan manhajar Twitter kadai.

Wani mai amfani da Twitter, Mehdi Shadan ne ya wallafa bidiyon a ranar 12 ga watan Disamba. A cikin bidiyon, an gano sabbin ma’auratan suna gasar marin junansu.

A cikin dan takaitaccen bidiyon wanda bai wuce tsawon sakan 19 ba, an gano inda amaryar ta fara shararawa mutumin mari a fuska kuma duk mutanen da ke wajen sun cika da mamakin abun da ta aikata.

Ma’aurata sun yi fada a ranar aurensu

Kan abun da ya haddasa marin mai kwance kunne, alamu sun nuna angon na ciyar da amaryar ta karfin tuwo sai ita kuma ta yi kokarin han shi.

Ta shararawa mutumin mari sannan shima ya rama lamarin da ya haddasa fadan da ya ja hankalin yan biki.

Mutanen da ke wajen sun gaggauta zuwa rabon fada domin dai ma’auratan sun shiga damben gaske a tsakaninsu.

An cire rawanin da ke kan ango a cikin haka kuma wurin gaba daya ya zama wani gidan dambe.

Bidiyon ya baiwa masu amfani da Twitter mamaki. A cikin martani ne wani mai suna @tbhnikhil ya ce: “An haliccesu daidai da junansu.”

Ba a bayyana a inda abun ya faru ba. Kalli bidiyon a nan.

A wani labari na daban, wani ango ya fasa auren budurwarsa bayan ya gano cewa tana da haihuwar yara har guda biyu amma fafur ta boye masa har zuwa ranar aurensu inda ya bankado abun da kansa.

Bala Baba Dihis wanda ya wallafa mummunan labarin a Facebook ya ce abun ya faru ne da wani abokinsa.

A cewar Baba, an shirya daura auren ne a ranar Asabar, 17 ga watan Disamba. Amaryar ta boyewa angon al’amarin amma sai ya gano da kansa.

Jama’a sun yi martani a kan al’amarin inda mutane da dama suka caccaki matar kan wannan babban kuskure da suka yi.

Da dama sun nuna mamakinsu cewa a danginta an rasa mai fada mata gaskiya domin dai boye al’amarin bai dace ba.

Duba nan: