Friday, May 31, 2024

Tsohon Gwamnan Jihar Adamawa Ya Fice Daga APC Zuwa PDP

Manyan Labarai

Duk da ziyarar da shugaba Buhari ya kai Yola, Tsohon gwamnan jihar Adamawa, Jibrilla Bindow, ya sauya sheka daga APC zuwa PDP.

Tsohon gwamnan jihar Adamawa da ya sauka ya ba Ahmadu Fintiri na yanzu, Sanata Jibrilla Bindow, ya tattara kayansa ya koma Peoples Democratic Party (PDP).

Channels tv ta rahoto cewa a halin yanzu Sanata Bindow na tare da kudirin gwamna mai ci, Umaru Fintiri na zarce wa zango na biyu a kan madafun iko.

Tsohon gwamna, wanda kafin wannan lokacin mamba ne a jam’iyyar All Prigressive Congress (APC) ya bayyana matakin da ya dauka ne ta bakin wakilansa.

Shugabannin kungiyoyi 250 da ke goyon bayan Jibrilla Bindow ne suka sanarwa gwamna Fintiri matakin tsohon gwamnan na sauya sheka tare da mara masa baya a zabe mai zuwa.

Da yake karin haske a dakin taron Banquet Hall da ke gidan gwamnati a Yola babban birnin jihar Adamawa ranar Litinin, shugabam wakilan Bindow, Abdullahi Bakari, ya ce sun kawo wannan ziyara ne bisa umarnin ubangidansu.

A cewar jagoran tafiyar, tsohon gwamnan ya umarci su isar da sakon yabo da godiya ga gwamna Fintiri bisa jajircewa wajen tabbatar da ya karisa ayyukan Alherin da ya zo ya taras a dukkan sassan jihar.

Bugu da kari, sun ayyana cikakken goyon bayansu ga dan takarar shugaban kasa a inuwar jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar.

Sun bayyana cewa tsohon mataimakin shugaban kasan ya kasance jagora nagari a wurinsu tsawon shekaru don haka akwai bukatar su mara masa baya ya cika burinsa na shugabancin Najeriya.

A wani labarin kuma Daya daga cikin ‘yan takarar da suka nemi tikitin APC, Okorocha Ya Fayyace Gaskiya Kan Batun Komawarsa PDP

Rahotannin cewa dan majalisar ya shiga jam’iyyar hamayyar ne bayan an gan shi a wani hoto tare da tsohon gwamna Emeka Ihedioha a wurin jana’izar daya cikin hadimansa, Pascal Uju.

Duba nan: