Thursday, May 30, 2024

Shugaban Jam’iyyar NNPP a Jihar Kaduna Ya Yi Murabus, Ya Sauya Sheka

Manyan Labarai

Shugaban New Nigeria Peoples Party, (NNPP), Ben Kure ya fice daga jam’iyyar bisa zargin wuce gona da iri da shiga sharo ba shanu na ɗan takarar gwamna, Sanata Suleiman Hunkuyi, ke yi a cikin gida.

Jaridar Punch ta rahoto cewa Mista Kure yace ya tattara kayansa ya bar jam’iyyar ne saboda, “Ba zai yuwu a samu kyaftin biyu a cikin jirgi ɗaya ba.”

A cewarsa, ya miƙa takardar yin murabus daga muƙaminsa ga babbar Sakatariyar NNPP ta ƙasa tun ranar 6 ga watan Disamba, 2022 bisa zargin Hunkuyi ya hana shi aikin Ofis ɗinsa don ɗaga kimar jam’iyya.

A ‘yan kwanakin nan tsohon shugaban jam’iyyar ba su ga maciji da ɗan takarar gwamnan Kaduna a inuwar NNPP da wasu daga cikin manyan jami’an jam’iyya a jihar.

Amma da yake hira da manema labarai ranar Alhamis, 15 ga watan Disamba, 2022 a Kaduna ya bayyana cewa ya yi nadamar zama shugaban jam’iyya a jihar.

Yace: “Bana fatan ko nan gaba wani abu ya sake haɗa mu da shugabannin jiha.”

Saboda haka ina mai sanar da ku da kuma ɗaukacin masoya na da abokanai na cewa na yi murabus daga muƙamin shugaban jam’iyyar NNPP reshen jihar Kaduna kuma daga yau na raba gari da jam’iyyar baki ɗaya.”

Zan ɗan sha iska na sarara tukunna na yi nazari kan abinda zan tunkara nan gaba da a siyasance daga bisani zan sanarwa al’umma inda da dosa.”

“Ina son faɗa muku cewa na aika wasikar murabus ɗina zuwa babbar Sakatariya ta ƙasa tun ranar 5 ga watan Disamba, 2022 amma suka rarrashe ni na jinkirta su shawo kan sabanin da aka samu.”

“Suka gayyace mu muka je aka zauna kuma a makon da ya gabata Sakatariyar ƙasa ta umarci mu shirya gangamin kamfe da tattakin nuna goyon baya a Kaduna karkashin jagoranci na amma Hunkuyi da sauran yan koransu suka shure umarnin uwar jam’iyya.”

Yayin da aka tuntuɓe shi domin jin ta bakinsa kan zargin wuce gona da iri da kokarin kwace iko da jam’iyya wanda tsohon shugaba ya ɗora masa, Hunkuyi ya maida martani a takaice da cewa, “Ba zan ce komai ba.”

Tushe: News Brief Hausa

Duba nan: