Friday, May 31, 2024

Saura Kwanaki Kadan a Yi Zabe, Dan Takarar Gwamnan PDP Ya Mutu, Meye Doka Ta Tanada?

Manyan Labarai

FCT, Abuja – Rahoton da muke samu daga majiya mai tushe na bayyana cewa, Allah ya yiwa dan takarar gwamnan PDP a jihar Abia rasuwa.

Farfesa Uche Ikonne ya rasu ne a asibitin tarayya da ke Abuja a yau Laraba 25 ga watan Janairu, kamar yadda rahoton Vanguard ya bayyana.

Labarin mutuwarsa na fitowa ne daga bakin dansa, Dakta Chikezie Uche-Ikonne.

Saura Kwanaki Kadan a Yi Zabe, Dan Takarar Gwamnan PDP Ya Mutu
Saura Kwanaki Kadan a Yi Zabe, Dan Takarar Gwamnan PDP Ya Mutu | Hot: Naija Naira

Dan nasa ya fitar da sanarwar da ke nuna jimami da rasuwar mahaifin, tare da bayyana irin fama da ya yi da rashin lafiya a nan gida Najeriya da ma kasar waje.

Ya zuwa yanzu jam’iyyar siyasa ta biyu mafi rinjaye a Najeriya; PDP bata yi martani game da mutuwar wannan mamba nata kuma wanda ta ba tikitin gwamna ba.

Ta yaya za a maye gurbinsa?

Yayin da dan takarar ya mutu, babban abin da ‘yan Najeriya za su fi mayar da hankali a kai shine; wanda zai gaje shi ganin yadda zaben ya karato.

Sabuwar dokar zabe da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanyawa hannu ta bayyana dalla-dalla yadda za a shawo kan al’amari irin wannan.

Dokar ta tanadi matukar dan takara ya mutu ko ya janye, to jam’iyya za ta sake gudanar da zaben fidda gwanin gwamna a cikin kwanaki 14.

A wani bangare kuma, an ce dokar ta tanadi cewa, kwamishinan zabe na kasa ne zai sanya lokacin yin zaben bayan duba da gamsuwa da mutuwar dan takara.

Hakan ya taba faruwa ne a Najeriya?

A yanayi mai kama da na Uche, a ranar 22 ga watan Nuwamban 2015 gabanin rantsar da Abubakar Audu a matsayin gwamnan Kogi bayan lashe zabe, Allah ya yi masa rasuwa.

Wannan lamari ya haifar da damuwa game da abin da ka iya biyo baya a jam’iyyar APC da ta lashe zaben shugaban kasa a shekarar.

A madadin sake zaben fidda gwani, jam’iyyar APC ta zabi Yahaya Bello, wanda shine na biyu a jerin wadanda suka fafata a zaben fidda gwani don maye gurbin gwamnan.

Sai dai, a wannan karon, an yi sauye-sauye a kundin zabe, kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya riga da ya sanya hannu kan dokar.

Abin da zai faru? Babu wanda ya sani, kasancewar PDP bata yi martani ba, kana hukumar zabe mai kanta bata ce komai ba.

Tushe: News Brief Hausa

Duba nan: