Friday, May 31, 2024

Na Zama Hajiyar Gida: Matashiya Ta Cika Da Farin Ciki Bayan An Daura Mata Aure, Bidiyonta Tana Farin Ciki Ya Yadu

Manyan Labarai

Wata matashiyar budurwa ta wallafa wani bidiyo a Instagram don nuna farin cikinta bayan an daura mata aure.

A bidiyon da ta wallafa a shafinta na Instagram mai suna @unique.aiphy, matashiyar mai suna Ifunanya Ochei ta ce rayuwar yanmatanci akwai matukar wahala.

Ifunanya ta ce ta ga ‘jalala’ lokacin da bata yi aure ba saboda mutane na amfani da ita wajen fadin munanan kalamai.

A yanzu da ta samu Allah ya yi mata gamon katar da aure da kuma kasancewa a cikin gidan mijinta, ta bayyana cewa burinta ya cika yanzu kuma tana cikin farin ciki.

A cewar Ifunanya, yanzu ta zama cikakkiyar matar gida kuma ta kan kasance cikin farin ciki idan ta farka ta ga mijinta.

Ta ce:

“Shekara daya bayan aurena, ina matukar mamaki wai da gaske na yi aure.”

Bidiyon da aka wallafa a ranar 30 ga watan Disamba ya yadu kuma ya haifar da martani daga masu amfani da Instagram.

Kalli bidiyon a nan

Jama’a sun yi martani

@ugokingsdonkil ta ce: “Lols! Kina da ban dariya fa Ify! Kwana biyu yar’uwa. Ina kewanki da yawa.”

@loistruly ta ce: “Kwarai. Mace mai karfin zuciya ko wacce bata damu da abun da jama’a ke fadi ba tana ganin kawai ta yi harkokin da ke gabanta shine kuma shi take yi. Imma ki yi ko kada ki yi, sai sun yi magana, don haka kawai ki yi abun da ya yi maki.”

Ba Zan Yi Soyayya da Wanda Ba Zamu Rika Jin Dadin Juna Ba, Jaruma

A wani labarin, shahararriyar jaruma ta shirin fina-finan Najeriya ta bayyana ra’ayinta game da wani batu da ake tattauna wa a kafafen sada zumunta wanda ya shafi soyayya.

Jaruma a masana’antar shirya-shirya fina-finan Nollywood da ke kudancin Najeriya, Nkechi Blessing, wacce ta yi fice tace ba zata yi soyayya da mutumin da bai waye ba ta bangaren amfani da albarkatun jikin mace.

Jarumar ta bayyana haka yayin da take fadar ra’ayinta kan batun soyayya babu jin dadin juna da ake tattauna wa a soshiyal midiya.

A cewar kyakkywar jarumar, ba zata shiga layin kalar wannan soyayyar ba wacce namiji ba zai rika kwanciya da ita suna sharholiyarsu ba, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Duba nan: