Thursday, August 31, 2023

Matashi Da Ya Ku’dance Ya Tuna Da Abokansa Da Suka Ci Kwakwa Tare, Ya Kai Masu Ziyara

Manyan Labarai

Wani matashi dan Najeriya ya taba zukata yayin da ya ziyarci abokansa da suka yi rayuwa tare a unguwar talakawa.

Da yake wallafa bidiyon ziyarar da ya kai unguwar talakawan a TikTok, mutumin ya bayyana cewa abokan nasa sun kula da shi tsawon shekaru da dama.

Yayin da yake martani ga wani mutum, ya ce ba mutane da yawa bane suka fahimci nauyin da ke tattare da zama dan fari daga gidan talakawa ba.

Ya ce ya yi yawancin rayuwarsa ne a unguwar talakawa kuma ba zai taba mantawa da mutanen da suka taimake shi ba a lokacin da abubuwa suka yi masa zafi a baya ba.

“Mutane da yawa ba za su fahimci wahalar da ke tattare da zama dan fari daga gidan talakawa ba…yawancin rayuwana na yi su ne tare da abokai a unguwar talakawa.”

Bidiyon ya nuno shi zaune a kasa tare da su yayin da suke hira cikin nishadi.

Mutane da dama sun yaba masa kan yadda ya tuna da abokansa kasancewar wasu da zaran sun samu arziki sai su manta wadanda aka yi gwagwarmaya tare.

Masu amfani da soshiyal midiya sun yi martani

SugeKid ya ce:

“Allah da ya yi maka zai yi mun nima.”

user90866529505094 ya yi martani:

“Ina fatan samun irin naka.”

user90866529505094 ya ce:

“Maigida ka albarkaci yaronka mana…koma nawa ne zai yi.”

Mark Smith ya ce:

“Ina fatan samun irin naka.”

Ango ya fasa auren budurwarsa bayan ya bankado wani sirri nata

A wani labari na daban, wani ango ya kekyashe kasa ya ce baya yi yayin da ake gab da daura masa aure da budurwarsa bayan ya bankado wani sirri da matar ke boye masa.

Matashiyar amaryar dai na da ‘ya’ya har guda biyu da ta haifa da wani mutum daban amma ta boye ta ki sanar da mai shirin zama angon nata har sai da ya gano lamarin da kansa.

Mutane da dama da suka yi martani a soshiyal midiya sun caccake ta tare da Allah wadai da wannan abu da ta aikata harma wasu na ganin danginta basu da tunani tunda har basu iya tursasa ta fada ma angon nata gaskiyar batu ba.

Duba nan: