Thursday, May 30, 2024

Magoya Baya Sun Nemi Atiku, Obi da Kwankwaso Su Janye Daga Takarar Shugaban Kasa a 2023

Manyan Labarai

Kasa da watanni biyu gabanin babban zaben shugaban kasa dake tafe a 2023, sananniyar kungiyar magoya bayan Bola Tinubu, Tinubu/Shettima Network (TSN) ta yi kira ga sauran masu neman zama shugaban kasa su janye wa dan takarar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Jaridar Daily Trust ta ce shugaban kungiyar TSN na kasa, Dakta Kailani Muhammad, ne ya yi wannan kira jiya Alhamis a wurin rantsar da shugabannin kungiyar na matakin kasa da kuma kaddamar da hedkwata a birnin tarayya Abuja.

Injiniya Kailani ya bukaci masu hangen zama shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar, na Labour Party, Peter Obi, na NNPP mai kayan marmari, Rabiu Musa Kwankwaso, da sauransu da su janye wa Bola Tinubu, su daina asarar karfin su da dukiyarsu a wurin kamfe.

A kalamansa ya ce:

“Mun san cewa kowane dan takara da ke hankoron kujerar shugaban kasa a Najeriya yana da cancanta daidai gwargwado amma Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya masu fintinkau wajen dace wa da matsayin.”

“Saboda haka abinda ya kamata shi ne su janye daga tseren zama shugaban kasa su mara masa (Tinubu) baya ya kai ga nasara.”

Idan baku manta ba manyan ‘yan takarar kujera lamba ɗaya a Najeriya irinsu, Atiku Abubakar na PDP, Peter Obi na LP da Rabiu Kwankwaso na NNPP sun jima suna nanata cewa sun shiga tseren ne domin su lashe zabe kana su ceto kasar nan daga kalubalen da ta tsinci kanta.

Zan Kwaci Kujerar Sanata a Zaben 2023 Da Karfin Tsiya, Gwamnan APC

A wani labarin kuma Gwamna David Umahi ya cika bakin cewa dole ga kwaci kujerar Sanatan Ebonyi ta kudu a zaben 2023 ko da karfin tsiya

Gwamna Umahi ya yi wannan furucin ne a mahaifarsa Uhuru da ke karamar hukumar Ohaozara ranar Laraba, 28 ga watan Disamba, 2022.

Ya kara cewa yana da kwarewa da gogewar da ake bukata na wakiltar mutane ba wai na Ebonyi ta kudu kaɗai ba, jihar baki ɗayanta da kabilar ibo kafataninta.

Duba nan: