Wata kyakkawar budurwa ta wallafa bidiyon lokacin da ta amsa tayin auren sahibinta wanda ya bukaci hakan daga gareta.
Wata matashiya mai suna Oyinda ce ta wallafa bidiyon inda ta bayyana cewa ta hadu da hadadden gayen ne a wajen wani bikin aure da ta halarta.
Budurwa za ta auri burin ranta
Soyayya ta kullu tsakaninsu kuma bayan shekaru uku, mutumin ya nemi auranta cikin yanayi na so da kauna kuma kebance su biyu.
A bidiyon mai sakan 20, matashin ya durkusa a gabanta don neman aurenta yayin da ta mika masa hannu domin karbar zoben.
Oyin da ta yiwa bidiyon take fa:
“Yan kwanaki da suka gabata, sahibina ya nemi na zama matarsa kuma shakka babu na amsa da eh!!! na kosa na ga lokacin da zan kare sauran rayuwata da shi. Allah ya mun gamon katar.”
Martanin jama’a
@Kulola Lynn ta ce: “Na so yadda kika saka takalman shan iska. Ina taya ku murna!”
@phartty tayi martani: “Na taya ku murna ‘yar uwa. Soyayya akwai dadi.”
@_wanjiku_mbugua ya ce: “Dakata ina mai shirin zama amaryar na da matukar kyau.”
@Katy Katy tayi martani: ”Akwai ban mamaki yadda hakan ya faru. Na taya ki murna.”
Hotuna: Budurwa Ta Sace Zuciyar Wani Matashi Bayan Ta Masa Sako a Whatsapp, Sun Shiga Daga Ciki
A wani labari mai kama da wannan, wata kyakkyawar budurwa ‘yar Najeriya wacce ta aikewa wani hadadden saurayi sako ta Whatsapp da misalin karfe 4:20 na asubahi a shekarar 2020 sun yi aure da wannan gayen.
A wata wallafa da ta yi a Twitter a ranar Asabar, 10 ga watan Disamba, matar mai suna Ugo ta bayyana cewa ta samu lambar mutumin ne a wani kungiyar yan Twitter da ke Whatsapp.
Ugo ta ce mutumin ya hadu matuka don haka ta yanke shawarar gwada sa’arta ta hanyar aike masa sako da asuban fari.
Ga mamakinta, ya yi mata martani ba tare da bata lokaci ba kuma tun daga nan soyayyarsu ta yi zurfi duk da fadi tashin da suke ta yi har dai ya yi mata tambaya.
Abun mamaki, a lokacin da suka hadu da mutumin a Whatsapp. Ugo ta ce tana jihar Borno inda take aikin bautar kasa na shekara daya.