Thursday, May 30, 2024

Kano: A dawo min da kudin fom ɗi na, tsohon ɗan takara ya faɗa wa jam’iyyar LP ta Peter Obi

Manyan Labarai

Kano – Tsohon mai neman takarar kujerar majalisar wakilai na tarayya ta Fagge a Kano, Osita, Nwankwo, a ranar Litinin ya bukaci a dawo masa da kudinsa N500,000 da ya biya shugabanin Labour Party, LP, tunda an bawa wani dan takarar kujerar.

A cewarsa, hakan ya biyo bayan rashin bashi tikitin takara da shugabannin jam’iyyar suka yi don ya wakilci Fagge, Kano a majalisar tarayya don ya gaza biya N5m don bashi tikitin, rahoton The Punch.

Ya ce:

“Na biya kudin a asusun Labour Party mai lamba 1021575052 da 20634382 a bankin UBA a ranar 6 ga watan Yulin 2022, N400 kudin fom sai kuma N100,000 kudin yafiya tunda ni ba dan jam’iyyar bane kafin zaben. Na kuma biya N100,000 a asusun mai bada shawara na shari’a duk a UBA, tare da hujjan biya.”

A cewarsa, an bukaci ya biya abin da ya ke da shi don tiktin, ya biya N500,000, amma jam’iyyar ta ce a’a, ta dage sai ya biya N3m na tikiti da N5m na yafiya, I Reporter Online ta rahoto.

Gazawar biyan N3m da N5m din yasa shugabannin jam’iyyar suka bawa wani Shuaibu Abubakar, wanda ya cika sharrudansu tikitin.

Don haka, Nwankwo ya ce:

“Ni rubuta wasika da shugabannin LP ina neman a dawo min da N500,000 tunda an bawa Abubakar tikitin, wanda ya cika ka’idarsu.

“Wata shida bayan wasika ta, babu amsa, shi yasa na ke amfani da wannan damar don neman a dawo min da kudi na, duba da cewa jam’iyyar ba ta da niyyar biya na kudin, duk da ta bawa wani tikitin.”

An dawo min da N90,000, saura N500,000, – Tsohon mai neman takara a LP a Kano

Amma, dan takarar mai neman hakinsa ya tabbatar jam’iyyar tuntuni ta dawo masa da N90,000 da ya biya na nuna sha’awar takara, yana mai cewa abin da ya yi sauea shine N500,000, don jam’iyyar ta kwatanta gaskiya da adalci.

“Don haka ina neman a dawo min da N500,000 cikin gagagwa don nuna adalci da gaskiya na jam’iyya,” in ji shi.

Martanin ciyaman din LP na Kano

An yi kokarin tuntubar ciyaman din jam’iyyar LP na Kano, Mohammed Raji don ji ta bakinsa amma bai amsa kirarsa ba kuma bai amsa sakon Whatsapp ba a yayin hada wannan rahoton.

Tushe: News Brief Hausa

Duba nan: