Wednesday, May 29, 2024

Jiga-Jigai da Mambobi 91,000 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a Jihar Buhari

Manyan Labarai

People’s Democratic Party (PDP) reshen jihar Katsina ta karbi ‘yan siyasa masu sauya sheka 92,000 daga jam’iyyar All Progressive Congress (APC) da wasu jam’iyyu.

Jaridar Vanguard ta tattaro cewa PDP ta yi maraba da dubbannin masu sauya shekar ne a wurin gangamin yakin nemna zaɓen da ta shirya dan takarar shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, ranar Talata a Filin wasan Muhammad Dikko.

Darakta Yaɗa labarai na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa ne ya sanar da haka a wurin taron. Yace mambobin APC 49,000 suka tattara kayansu suka dawo PDP a shiyyar Katsina.

Haka zalika ya bayyana cewa ‘yan siyasa 23,000 suka rungumi jam’iyyar laima a shiyyar Funtuwa yayin da wasu 19,000 suka bi sawunsu a shiyyar Daura, jumulla mutane 91,000 kenan daga shiyyoyin jihar guda uku.

Sanata Dino Melaye ya ce:

“Maza da mata ku suarara, ina son sanar muku da abun farin ciki a takaice cewa yau mun karɓi masu sauya sheka daga shiyyoyin Katsina guda uku. Daga shiyyar Daura mun sami mutane 19,000 da suka canza sheƙa kuma sun samu wakilcin Alhaji Yahaya Kwande.”

“Daga shiyyar Funtuwa muna da mutane 23,000 da suka ɗauki matakin shigowa PDP kuma sun samu wakilcin Alhaji Baba Yale Yaro.  A shiyyar Katsina kam mun samu mambobin APC 49,000 da suka sauya sheka bisa jagorancin Alhaji Aminu Lawal Mani.”

“Amma babban wanda muka samu nasara ya sauya sheka daga APC zuwa PDP shi ne tsohon Sakataren gwamnatin Aminu Bello Masari na nan jihar Katsina watau Mustapha Inuwa.”

Da yake maraba da dubbannin masu sauya shekar a hukumance, shugaban PDP na ƙasa, Iyorchia Ayu, ya yi wa mutanen barka da zuwa inuwar jam’iyyar laima.

Ya bayyana cewa sun yi tunanin mai kyau kuma cikin wayewa na haɗa karfi da babbar jam’iyyar adawa PDP a kokar<nta na ceto kasar nan daga mulkin APC.

A wani labarin kuma Daraktan yakin neman zaben Peter Obi na kasa, Doyin Okupe, ya yi murabus

Dakta Okupe, tsohon hadimin tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, yace ya ɗauki wannan matakin ne domin ba ya son wani abu daban da ya shafi rayuwarsa ya ɗauke masa hankali.

Wannan na zuwa ne awanni bayan Kotu ta kama sa da hannu dumu-dumu a laifukan da suka shafi halatta kuɗin haka, ta yanke masa hukunci.

Tushe: News Brief Hausa

Duba nan: