Saturday, June 1, 2024

Jam’iyyar PDP Ta Dakatar da Kakaki A Jihar Gombe, Ya Yi Murabus

Manyan Labarai

Rigingimun babbar jam’iyyar adawa ta ƙasa Peoples Democratic Party (PDP) na ƙara tsananta yayin da a jihar Gombe jam’iyyar ta sanar da dakatar da mai magana da yawunta.

Jaridar Pmnews Nigeria ta ruwaito cewa jam’iyyar PDP reshen Gombe ta tabbatar da ɗaukar matakin dakatarwa kan mai magana da yawunta, Mista Murtala Usman, bisa zargin da take masa na cin amana.

Sakataren PDP na jiha, Alhaji Adamu Abubakar ne ya sanar da matakin a wata sanarwa da ya sa wa hannu kuma ya raba wa manema labarai ranar Alhamis a birnin Gombe.

Sakataren ya ce:
“A matsayinsa na jami’in hulɗa da jama’a na PDP wanda ya dace aga yana musayar yawu da kowa don kare muradan jam’iyya sai ya ɓushe da wasu halaye abin zargi da mamaki duba da manufa da kokarin farfaɗowar jam’iyya.”
“Bisa haka muna masu sanar da al’umma cewa duk wanda ya kulla wani kasuwanci ko wata yarjejeniya da shi da sunan PDP to ya sani ya yi haka ne bisa karan kansa babu ruwan jam’iyyar mu.”

Da yake martani a wata hira da wayar salula, Murtala Usman ya tabbatar da cewa an kawo masa takardar dakatarwa ranar Alhamis da ta gabata.

Amma a bayanansa yace dama ya jima yana kokarin rubuta wasikar aje aiki daga mukamin mai magana da yawun PDP kafin a kawo wannan lokacin na dakatar da shi.

A cewarsa tun da an yi haka bayan dakatarwar da aka masa shi a halin yanzu ya yi murabus daga kujerar mai magana da yawun jam’iyya amna ba inda zai je yana nan a matsayin mamban PDP.

Bugu da kari ya tabbatar da cewa idan ma ya yanke wata shawara ta daban zai sanar da al’umma nan ba da jimawa ba.

Ya jaddada cewa har yanzun yana nan kamar yadda kowa ya san shi da kokari da jajircewa na ganin an sake gina jam’iyyar PDP domin ta koma mulki a 2023.

A wani labarin kuma Jiga-Jigai da Mambobi 91,000 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a Jihar Buhari

Ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya gudanar da yakin neman zaɓensa a jihar Katsina dake arewa maso yammacin Najeriya.

Gangamin kamfen ya zo da kafar dama inda yayin taron babbar jam’iyyar adawa ta ƙasa ta yi lale marhabun da sauya shekar mambobi sama da 90,000 na wasu jam’iyyu zuwa PDP a shiyyoyin jihar uku.

Tushe: News Brief Hausa

Duba nan: