Saturday, June 1, 2024

Hotuna: Budurwa Ta Sace Zuciyar Wani Matashi Bayan Ta Masa Sako a Whatsapp, Sun Shiga Daga Ciki

Manyan Labarai

Wata kyakkyawar budurwa ‘yar Najeriya wacce ta aikewa wani hadadden saurayi sako ta Whatsapp da misalin karfe 4:20 na asubahi a shekarar 2020 sun yi aure da wannan gayen.

A wata wallafa da ta yi a Twitter a ranar Asabar, 10 ga watan Disamba, matar mai suna Ugo ta bayyana cewa ta samu lambar mutumin ne a wani kungiyar yan Twitter da ke Whatsapp.

Ugo ta ce mutumin ya hadu matuka don haka ta yanke shawarar gwada sa’arta ta hanyar aike masa sako da asuban fari.

Aure ya kullu a sanadin Whatsapp

Ga mamakinta, ya yi mata martani ba tare da bata lokaci ba kuma tun daga nan soyayyarsu ta yi zurfi duk da fadi tashin da suke ta yi har dai ya yi mata tambaya.

Abun mamaki, a lokacin da suka hadu da mutumin a Whatsapp. Ugo ta ce tana jihar Borno inda take aikin bautar kasa na shekara daya.

Ta ce ta koma Enugu inda yake da zama don ta kasance kusa da shi, amma ta bayyana hakan a matsayin mataki mai matukar hatsari. Sai kawai komai ya tafi daidai.

Cikin farin ciki, Ugo ta shawarci sauran mata da su dunga aikewa maza sakonni idan bukatar yin hakan ta taso.

Ugo ta ce:

“Yan shekaru a jere, ya tambaya ni kuma na ce eh har zuuciya. Ina farin cikin yin rayuwa da mutum mafi daraja. Darasin da ke cikin labarin: Ki aika sakon yar’uwa.”

Martanin mutane

@CollinsObekp ya ce:

“Kusan haka labarina yake, kawai dai namu ya faru ne a dan kankanin lokaci. A halin da ake ciki, dawowa na daga gareji kenan inda na rakata bayan yawon amarcinmu. Mun fara daga wajen sharhi a Facebook. Na taya ku murna.”

@lisaoleka  ta ce:

“Na karanta irin wannan da dama a manhajar nan fa…A karshe ta iya kasancewa mijina na nan.”

A wani labarin, mun kawo cewa soyayya babu ruwanta da kudi, sura ko kuma kyau. Da zaran zukata biyu sun hadu basa ganin kowa da komai sai junansu.

Hakan ce ta kasance a bangaren wasu ma’aurata wadanda ko kusa basu yi kamanceceniya ta wajen sura ba.

Yayin da angon ya kasance dogo mai ji da tsaye lamba daya, matar ta kasance yar tsirit gajeruwa a kasa. Sai dai hakan bai hana su shuakin junansu ba.

Duba nan: