Monday, August 28, 2023

Gwamna Ganduje Zai Rattaɓa Hannu a Rataye Sheikh AbdulJabbar

Manyan Labarai

Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, Khadimun Islam yace a shirye yake ya sa hannu a zartar da hukuncin rataya da Kotu ta yanke wa Sheikh AbdulJabbar Kabara bayan kama shi da laifin ɓatanci ga Annabi Muhammad SAW.

Jaridar Aminiya Dailytrust tace kwamishinan shari’a na jihar Kano, Lawan Musa ne ya sanar da haka yayin da aka nemi jin ta bakinsa kan hukuncin da babbar Kotun shari’a ta yanke.

Tun a watan Yuli na shekarar 2021, gwamnatin jihar Kano ta maka Shehin Malamin a gaban Kotu kan maganganun da yake yi a karatuttukansa na zindiƙanci wanda ka iya tunzura jama’a.

Shin gwamna Ganduje zai sa hannu a Hotuncin Rataya?

Kwamishinan Shari’a, Lawan Musa ya ce:

“Mai girma gwamna bai sauya daga matsayarsa ba game da rattaba hannu kan wannan hukunci. Haka zalika bai sauya shawara kan matsayarsa na sa hannun kan hukuncin wanda ya kashe Hanifa ba.”

“Akwai matakan da ya dace a doka a bi tukunna amma a ɓangaren gwamna a shirye yake da zaran an kawo masa zai sanya hannu a kai.”

Kwamishinan ya kara da bayyana cewa babu wanda zai karya doka kuma ya wanye lafiya, inda a cewarsa za’a ɗauki dukkanin matakan da suka dace.

“Mun kai ƙarar Malam Abduljabbar gaban Kotu ne domin ba shi duk wata dama da yanci da ya kamata ya kare kansa.”

“Kuma muna godiya ga Allah Kotu ta gamsu da hujjojin da muka gabatar a kan zargin da ake masa, kuma ta yanke hukunci dai-dai da abin da ya aikata.”

Bugu da ƙari, Lawan Musa ya ce a yanzu Kotu ta wanke gwamnati kuma hukuncin da ta yanke ya ƙara tabbatar da cewa babu wani da ya fi karfin doka.

News Brief Hausa ta fahimci cewa a ranar Alhamis, 15 ga watan Disamba, 2022, mai shari’a Ibrahim Sarki Yola, ya yanke wa Sheikh AbdulJabbar Nasiru Kabara hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Haka zalika Alkalin ya kuma umarci a kwace masallatai biyu da dukkanin Litattafan Malamin.

Tushe: News Brief Hausa

Duba nan: