Wednesday, May 29, 2024

EFCC Ta Kama Manajan Banki a Abuja Da Ya Boye N29m Na Sabbin Kudi

Manyan Labarai

Abuja – Hukumar yaki da rashawa na EFCC ta kama wani babban manajan gudanarwa na wani banki a Abuja da laifin yin sama da fadi da N29m wanda ya janyo karancin kudi a ATM.

 

An kama manajan da kudaden ne a rumbun bankin kuma ya ki yin loda ATM din duk da cewa akwai sabbin kudin, rahoton Daily Trust.

EFCC ta kama manajan banki
An kama manajan banki a Abuja kan boye N29m. Hoto: Daily Trust

Kan a tafi da mutumin domin yi masa tambayoyi. Ma’aikatan EFCC sun ba da umarnin loda duk na’urorin ATM da kuɗi ga kwastamomi da kan kanta.

 

Wannan ya kawo farin ciki mutuka kasancewar sun jima a layi ba tare da samun sababbin kudin ba. An gudanar da aikin lafiya.wannan ya faru kan a tisa keyar manajan.

Shugaban yada labarai na EFCC Wilson Uwujaren ne ya fitar da sanarwa a ranar Litinin, Sahara Reporters ta rahoto.

Wilson Uwujaren na EFCC ya bayyana cewa sun gano cewa wasu bankuna na yin zagon kasa ga manufofin gwamnati. An gano hakan ne a yayin ziyarar da suke yi bankuna.

 

Hukumar na duba rumbunan bankunan ne don ganin ko da gangan suke kin fitar da sabbin takardun kudin.

Ya ce:

 

“EFCC ta binciki rassan bankuna 5 a Abuja ranar Litinin. Haka kuma EFCC na gudanar da irin wannan binciken a wasu yankunan kasar nan.”

Uwujaren ya bayyana cewa za a ci gaba da gudanar da irin wannan binciken har sai an dawo da tsarin banki kamar yadda aka saba.

Ya ce:

 

“Idan kana samun matsala wajen samun kudaden bankinka kuma kana zargin ana aikata ba daidai ba, tuntubi hukumar domin neman taimako.”

 

Duba nan: