Thursday, August 31, 2023

Daraktan Yakin Neman Zaben Peter Obi a 2023 Ya Yi Murabus

Manyan Labarai

Dakta Doyin Okupe, darakta janar na kwamitin yakin neman zaben ɗan takarar shugaban kasa a inuwar Labour Party, Peter Obi, ya yi murabus daga muƙaminsa.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa ya ɗauki wannan matakin ne biyo bayan samun hannunsa a badaƙalar kuɗin makamai a tsohuwar gwamnati da halasta kuɗin haram.

Okupe ya sanar da batun yin murabus dinsa ne a wata wasika da ya aike wa tsohon gwamnan Anambra kuma mai neman kujera lamba ɗaya a Najeriya, Peter Obi, ranar 20 ga watan Disamba, 2022.

Tsohon hadimin tsohon shugaban kasan yace ya yi sadaukarwa mai girma a kwamitim yakin neman zaben LP domin kar wani abu da ya shafi rayuwarsa ta kai da kai ya ɗauke masa hankali, dan haka ya yanke shawarin sauka daga mukamin.

Murabus ɗin Okupe na zuwa ne awanni bayan Kotu tace ta kama shi da hannu dumu-dumi wajen aikata laifuka 26 da suka shafi halatta kudaden haram.

Idan baku manta ba, tsohon mashawarci na musamman kan harkokin midiya ga tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, an kama shi da laifin karkatar da kuɗin makamai na Ofishin NSA.

Wata babbar Kotun tarayya mai zama a Abuja, yayin da take yanke hukunci tace ta kama Okupe da hannu a tuhuma daga lamba ta 34 zuwa 59 daga cikin tuhume-tuhumen da hukumar yaki da cin da rashawa EFCC ta gabatar a kansa.

Haka zalika Alƙalin kotun mai shari’a Ijeoma Ojukwu, ta sa soso da sabulu ta wanke shi daga tuhumar farko zuwa ta 33 waɗanda suke da alaƙa da cin hanci da rashawa.

Da yake jawabi kan cigaban, Peter Obi, a ranar Litinin yace kama Okupe da laifi ba zai shafi halayyarsa ko ya dakatar da shi daga yunkurin zama shugaban kasa a babban zaben 2023 mai zuwa.

A wani labarin kuma Matar Dan Takarar Shugaban Kasa Na PDP Ta Tafka Baranbarama a Sabon Bidiyo

Uwar gidan tsohon mataimakin shugaban ƙasa ta bi sahun maigidanta ta girgiza Intanet da wani sabon subutar baki da ba’a taba yi ba tun fara kamfe.

Tun bayan fara kamfe harshen manyan ‘yan takara suka fara kucce wa kama da Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC da Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP.

Tushe: News Brief Hausa

Duba nan: