Wednesday, May 29, 2024

Dan China Da Ake Zargi Da Kisan Ummita Ya Ce Ya Kashe Mata Miliyan N60

Manyan Labarai

A ranar Laraba, 11 ga watan Janairu ne mutumin kasar Chinan nan mai suna, Frank Geng Quangrong, wanda ake zargi da kisan masoyiyarsa yar jahar Kano Ummukulsum Sani, wacce aka fi sani da Ummita, ya fara kare kansa a kotu.

Quangrong ya sanar da kotu cewa shi Musulmi ne kuma ya na aiki a wani kamfanin tufafi a kasuwar Kantin Kwari da ke jahar Kano.

Wanda ake zargin ya bayyana cewa sun hadu da marigayi Ummita ne a shekarar 2020, bayan da ta samu lambar wayarsa a wajen wata kawarta, inda ta nuna tana son shi kuma za ta aure shi.

Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa dan Chinan ya ce bayan ya amince da ita, sai su ka fara soyayya, inda ta dungi karbar kudade daga wajensa.

Ya kara da cewa “haka na dungi bata duk abinda ta roke ni sabo da bana son na bata mata rai. Na kashe mata kimanin Naira miliyan 60,”

Ya Kara da cewa har gida na miliyan 4 ya sai mata, amma sai ji yayi ta yi aure, inda hakan ya bata masa rai ya koma Abuja da zama.

“Amma duk da haka ta dungi kira na tana hira da ni ta WhatsApp. Bayan nan ta ce min auren ya mutu, shine soyayyar ta mu ta dawo.”

A cewar sa, wata rana ta tambaye shi kudi shi kuma ya ce bashi da shi, shi ne Ummita ta yi fushi da shi har ta dena kula shi.

“Kawai sai ta ce min ta samu wani saurayin, har ma ta turo min hoton ta da shi sabon saurayin nata, lamarin da ya fusata ni,” in ji shi

Alkalin kotun, Sanusi Ado Ma’aji, ya bada umarnin a ci gaba da tsare Quanrong a gidan yari, sannan ya dage zaman zuwa gobe Alhamis domin ci gaba da sauraron kariya.

 

Duba nan: