Thursday, November 7, 2024

Da Dumi-Dumi: Wasu Tsageru Sun Sheke Dan Takarar Majalisa a 2023

Manyan Labarai

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin makasan da ake É—aukar haya ne sun halaka É—an takarar mamba mai wakiltar Æ™aramar hukumar Onuimo a majalisar dokokin jihar Imo karkashin inuwar jam’iyyar Labour Party, Christopher Elehu.

Jaridar Punch ta rahoto cewa ba ya ga raba shi da rayuwarsa, ‘yan bindiga sun cinna wa gidansa wuta kuma suka yi kaca-kaca da wasu kadarorinsa ciki har da Babur.

An tattaro cewa waÉ—anda ake zargi sun kai wannan mummunan farmaki kan É—an takarar ne da safiyar Jumu’a kuma sun kwashe awanni biyu suna harbe-harbe.

Wasu rahotanni sun bayyana cewa maharan, wadanda alamu suka nuna sun fusata, sun shiga gidajen ‘yan siyasan yankin amma suka taras ba su nan.

Wata majiya da ta nemi a sakaya bayananta ta tabbatar da kashe É—an takarar, inda ta ce:

Sun kashe Christopher Elehu, wanda aka fi sani da Wasco. Har zuwa lokacin mutuwarsa ya kasance ‘dan takarar majalisar jiha a mazaÉ“ar karamar hukumar Onuimo.”

“Sun kutsa cikin gidansa lokacin kowa ya shiga gida ya kwanta bacci kuma sun buÉ—e wuta na tsawon awanni biyu ba tare da an kawo É—auki ba.”

“Sun sheke mutumin kana suka Æ™one gidansa, duk da haka ba su hakura ba sai da suka yi kaca-kaca da kadarorinsa. Gawar na can kwance a saman Siminti  da mutane suka je gane wa idonsu sun ga alamun raunukan wuka a jikinsa.”

News Brief Hausa ta gano cewa wannan kisan ɗan siyasan ya zo ne kwanaki 10 bayan wani ɗan takara a inuwar LP a ƙaramar hukuma mai makwaftaka da nan watau Okigwe, Chukwunonye Irouno, ya mutu farat ɗaya ba zato ba tsammani.

Irouno, wanda aka yi tsammanin zai jagoranci gangamin yakin neman zaɓen shugaban ƙasa na Peter Obi, ya mutu ne a daren da ya kasance kwana ɗaya gabanin gangamin.

Da farko an yi gaggawar kai shi babbar cibiyar lafiya ta gwamnatin tarayya (FMC) da ke Owerri, a can ne Likitoci suka tabbatar da rai ya yi halinsa.

Har zuwa yanzun da muke kawo muku wannan rahoton rundunar ‘yan sanda reshen jihar Imo ba ta fitar da wata sanarwa game da kashe É—an takarar majalisa na LP ba.

Tushe: News Brief Hausa

Duba nan: