Babbar jam’iyyar hamayya ta ƙasa watau PDP ta dakatar da Chimaroke Nnamani, Sanata mai wakiltar mazabar Enugu ta yamma a majalisar dattawan Najeriya.
Mai magana da yawun PDP, Debo Ologunagba, shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar da daren Jumu’a, rahoton The Cable ya tabbatar.
Ya ce jam’iyya ta ɗauki matakin dakatarwa kan Sanata Nnamani da wasu kusoshin jam’iyya Bakwai.
Ologunagba ya ce PDP ta cimma wannan matsaya ne bayan ta yi nazari mai tsawo kan yadda harkokin jam’iyya ke tafiya a sassan kasar nan bisa la’akari da kundin dokokin da aka kafata a kai.
Ya bayyana jerin sunayen sauran mutanen da aka dakatar da suka haɗa da, Ayeni Funso (Ekiti ta arewa), Ajijola Lateef Oladimeji (Ekiti ta tsakiya), Emiola Adenike Jennifer (Ekiti ta kudu II), da Ajayi Babatunde Samuel (Ekiti ta arewa II).
Sauran su ne, Olayinka James Olalere (Ekiti ta tsakiya), Akerele Oluyinka (Ekiti ta arewa I), da kuma Fayose Oluwajomiloju John (Ekiti ta tsakiya I). Kakakin PDP yace matakin zai fara aiki ne nan take.
Sanarwan ta ce:
“Bayan dogon nazari da kwamitin ayyuka (NWC) na PDP ta kasa ya yi duba yadda harkokin jam’iyya ke tafiya da dogaro da kundin dokokin da aka wa garambawul, ya amince da dakatar da Sanata Chimaroke Nnamani daga jihar Enugu da Chief Chris Ogbu na Imo daga yau Jumu’a 20 ga watan Janairu, 2023 kan zargin yi wa jam’iyya zagon ƙasa.”
“Jam’iyar PDP na rokon shugabanni, masu ruwa da tsaki da tawagar magoya baya a dukkan sassan ƙasar nan da su ci gaba da zama tsintsiya ɗaya kuma su maida hankali ga babban aikin ceto da gina kasar nan da jam’iyyar ta sa a gaba.”
Duk da kasancewarsa mamba a jam’iyyar PDP, Sanata Nnamani, ya fito fili ya ayyana goyon bayansa ga Bola Ahmed Tinubu, ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar APC.
A wani labarin kuma Tsohon Gwamnan Jihar Adamawa Ya Fice Daga APC Zuwa PDP
Tsohon gwamnan jihar Adamawa da ya sauka ya ba Ahmadu Fintiri na yanzu, Sanata Jibrilla Bindow, ya tattara kayansa ya koma Peoples Democratic Party (PDP).