Monday, August 28, 2023

Da Dumi-Dumi: Babban Banki CBN Ya Kara Yawan Kuɗin Cirewa Duk Mako

Manyan Labarai

Babban bankin Najeriya (CBN) ya kara yawan mafi yawan kuɗin da ɗaiɗaikun mutane da kungiyoyi zasu cire duk mako bayan an yi wa sabon tsarin rubdugu.

The cable ta tattaro cewa a CBN ta sauya tsarin da cewa kowane mutum ɗaya na da ikon zare mafi yawa N500,000 a duk mako daga asusun bankinsa, yayin da kungiyoyi zasu iya cire miliyan N5m.

Wannan na ƙunshe a wata sabuwar sanarwa da babban bankin ya fitar ranar Laraba ɗauke da sa hannun Haruna Mustapha, daraktan sashin sa ido kan harkokin banki.

Mako biyu kenan da CBN ta sanar da sabon tsarinta wanda ya kayyade adadin kuɗin da kowane ɗan Najeriya zai cire N100,000 duk mako, N500,000 duk mako ga kungiyoyi.

Baya ga haka, Bankin ya rage adadin kuɗin da kowa zai iya cirewa a ATM da kuma wurin ‘yan kasuwa masu POS zuwa N20,000 kowace rana.

Wannan sabon tsari ya ta da kura a sassan ƙasar nan, yan Najeriya suka yi ta cece-kuce kan lamarin.

Yayin da wasu suka bayyana cewa tsarin zai murkushe kananan ‘yan kasuwa, wasu kuma sun yi marhabun da tsarin wanda a cewarsu zai kara habaka hada-hada ba tare da takardun kuɗi ba kuma zai rage yawan kuɗin dake yawo a hannun jama’a.

Ko meyasa babban bankin ya janye sabon tsarin?

A halin yanzun matsin lamba ta jawo babban bankin ya soke sabon tsarin da ya ɓullo da shi.

CBN yace ya ɗauki wannan matakin bayan sauraron korafe korafe daga masu ruwa da tsaki daga dukkan sassan ƙasar nan.

Idan baku manta ba lamarin dai ya haddasa kace-nace a tsakanin ‘yan Najeriya har ta kai ga majalisar wakilan tarayya ta aika da gayyata ga gwamnan CBN.

A wani labarin kuma Daraktan Yakin Neman Zaben Peter Obi a 2023 Ya Yi Murabus

Bayan kama shi da hannu dumu-dumu da laifukan da suka haɗa da kwamushe kuɗin al’umma, tsohon hadimin Jonathan, Doyin Okupe, yace ya hakura da mukamin daraktan kamfen jam’iyyar LP na kasa.

A wata sanarwa da ya fitar, Mista Okupe yace duk da ya zuba lokacinsa da hannun jari a kamfen LP amma yana ganin bai kamata abinda ya shafi rayuwarsa ya taba al’amuran Peter Obi ba.

Duba nan: