Thursday, May 30, 2024

Da Dumi-Dumi: Atiku Abubakar Ya Dawo Gida Najeriya

Manyan Labarai

Mai neman zama shugaban kasa a inuwar jam’iyar Peoples Democratic Party watau PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya dawo gida Najeriya daga kasar Burtaniya.

Tsohon hadimin shugaban kasa, Reno Omokri, shi ne ya wallafa bidiyon isowar tsohon mataimakin shugaban ƙasan a shafinsa na dandalin sada zumunta Tuwita ranar Jumu’a 13 ga watan Janairu, 2023.

A cikin bidiyon an hangi Atiku tare da gwamnan jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel, gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal da tsohon Sanata daga jihar Kogi, Sanata Dino Melaye.

Sauran jiga-jigan babbar jam’iyyar hamayya ta kasa da aka hanga a cikin tawagar dan takarar shugaban kasan su ne, tsohon shugaban PDP, Uche Secondus, tsohon ministan sufurin jiragen sama, Osita Chidoka da tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki.

Bayan tafiyar Atiku kasar waje, ‘yan Najeriya sun yi ta cece-kuce kan inda tsohon mataimakin shugaban kasan ya shiga.

Haka zalika an kai ruwa rana tsakanin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na manyan jam’iyyu biyu APC da PDP kan dalilin ficewar Atiku daga Najeriya zuwa kasar waje.

PCC-PDP ya karyata zargin da ake cewa Atiku ya tafi duba lafiya ne, inda a cewar Dino Melaye, tsohon mataimakin shugaban kasar ya tafi hutu ne Dubai kuma zai wuce Landan amsa gayyata.

A ranar Litinin da ta gabata, aka wallafa Hotunan Atiku yayin da ya isa Landan amma duk da haka takwaransa na jam’iyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya nemi dan takarar PDP ya fito ya bayyana rahoton Asibiti.

A wani labarin kuma Tsohon gwamnan jihar Adamawa Bindow ya sauya sheka daga APC zuwa PDP

Tsohon gwamnan jihar Adamawa da ya sauka ya ba Ahmadu Fintiri na yanzu, Sanata Jibrilla Bindow, ya tattara kayansa ya koma Peoples Democratic Party (PDP).

Tsohon gwamna, wanda kafin wannan lokacin mamba ne a jam’iyyar All Prigressive Congress (APC) ya bayyana matakin da ya dauka ne ta bakin wakilansa.

Duba nan: