Wednesday, May 29, 2024

Da Dumi-Dumi: An Shiga Ganawa da Shugabannin Bankuna Don Duba Yiwuwar Dage Wa’adi

Manyan Labarai

Yanzun nan kwamitin majalisar wakilai da ke lura da batun kudi ya shiga ganawa da shugabannin bankuna a Najeriya.

An ce ganawar za ta duba dalilai da suka sa har yanzu kudade basu wadata ba a hannun mutane yayin da wa’adin CBN ke kara gabatowa.

A tun farko, an gayyaci shugabannin ne domin ba da bahasi da samawa ‘yan Najeriya sauki game da sabbin Naira da kuma yadda za a shigar tsoffi.

Hakazalika, tattaunawar za ta yi duba ga yiwuwar dage wa’adin da CBN ya shar’anta na daina amfani da tsoffin kudade.

Ku dakaci karon haske…

Duba nan: