Thursday, August 31, 2023

Buhari da CBN Sun Sauya Fasalin Naira Ne Don Kawo Tsaiko Ga Zaben 2023, Inji Bola Tinubu

Manyan Labarai

Jihar Ogun – Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ya zargi gwamnatin Najeriya da kitsa hanyar kawo tsaiko ga zaben 2023 da ke tafe.

Tinubu ya fadi haka ne a wani taron kamfen na APC da aka gudanar a jihar Ogun a ranar Laraba 25 ga watan Janairun 2023, rahoton Punch.

A cewarsa, tsada da karancin man fetur da ake fuskanta a Najeriya ba komai face yadda wasu tsirarun mutane a Najeriya ke son ganin an samu matsala bai hau mulki ba.

Bola Tinubu
Bola Ahmed Tinubu. Hoto: The Punch

A lokuta da dama, Tinubu kan nuna yana kaunar hawa kujerar shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda ta hakan yake nuna bacin rai da yin maganganu masu rudarwa.

Za mu yi tattaki zuwa rumfunan zabe

Da yake jawabi, ya ce ko da an hana tare da boye man fetur a kasar nan, masoyansa za su fito kwai da kwarkwata domin kada masa kuri’a a ranar 25 ga watan Fabrairu.

A cewarsa, mutane a shirye suke su yi zabe, amma ana kokarin siyasantar da harkar man fetur a kasar.

Ya bayyana mafita ga tsadar mai da karancinsa, inda yace yana hawa mulki zai tabbar da ba a sake samun matsalar mai ba a Najeriya.

Tsohon gwamnan na Legas ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi hakuri, kana kada su bari a haramta musu yin zabe haka sidddan.

Sauya zubin Naira wani shiri ne na kawo tsaiko ga zabe, inji Tinubu

A bangare guda, Tinubu ya zargi gwamnatin Najeriya da yin mai yiwuwa don ganin an samu tsaiko ta hanyar dagula lissafin kasar wajen sauya fasalin Najeriya.

A haka ne yace, duk wadannan abubuwan ba za su sa ya sare ba, kuma kada ‘yan Najeriya su rudu da da duk wata manakisa da ake shiryawa don ganin an dage zaben 2023.

Ba za a dage zabe ba

A wani labarin kuma, hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta ce babu batun dage zaben 2023 balle soke shi, rahoton Vanguard.

Batun na fitowa ne daidai lokacin da ‘yan Najeriya ke nuna damuwa ganin yadda al’amarin tsaro ke kara lalacewa a kasar.

INEC ta ce ta kammala shiri, don haka ne ma ta gayyaci shugabannin jam’iyyu don nuna musu halin da ake ciki na adadin masu kada kuri.

Tushe: News Brief Hausa

Duba nan: