Wata kyakkyawar budurwa ta wallafa wani bidiyon zolaya a TikTok inda ta tunkari wani matashi sannan ta bukaci lallai ya furta mata soyayya.
Matashiyar mai suna Phoebe ce ta wallafa bidiyon kuma zuwa ranar Lahadi, 18 ga watan Disamba, ta samu mutum 428k da suka kalla.
A bidiyon, Pheobe ta tunkari wani bawan Allah da bata sani ba daga nesa sannan ta saka masa ihu.
Ta ci gaba da nanata bukatarta na neman mutumin yace yana sonta amma sam bai nuna yana ra’ayinta ba.
Bata yi masa ba kuma ya fito karara ya fada mata amma ta nace sai dai ya biya mata bukatarta.
Lamarin wanda alamu sun nuna zolaya ne karara ya wakana ne a wani wurin shakatawa.
Bidiyon ya haifar da martani a TikTok inda aka shawarci budurwar da ta yi hankali da irin wannan zolayar domin ana iya haduwa da bacin rana.
Kalli bidiyon a nan:
https://www.tiktok.com/@justphoebe___/video/7178010355212340486
Martanin jama’a
@Victory Robert ta ce: “Kuma a haka ta sami masoyi, daga baya sun fara magana sannan suka ci gaba da rayuwa cikin farin ciki.”
@Sampizzy ya yi martani: “Mutumin da bashi da tabbacin samun abincin rana. Shine za ki dunga zolaya.”
@Samson Victor ya ce: “Zolaya ya kai kaina wannan zai fasa mun waya.”
@Demiladesmart23 ya yi martani: “Kuma a haka ne na hadu da mahaifiyarki·”
@kesseky ya ce: “Dan Allah na roke ki ba kowa ke da nutsuwa ba. Mutumin nan baya dariya ko kadan.”
@faith ta ce: “baaba ina son yarinyar nan.”
@commentator ya yi martani: “mutum bai ci abinci ba tsawo kwana 2 kin ce ya bi ki.”
A wani labarin, wata kyakkawar budurwa ta wallafa bidiyon lokacin da ta amsa tayin auren sahibinta wanda ya bukaci hakan daga gareta.
Wata matashiya mai suna Oyinda ce ta wallafa bidiyon inda ta bayyana cewa ta hadu da hadadden gayen ne a wajen wani bikin aure da ta halarta.
Soyayya ta kullu tsakaninsu kuma bayan shekaru uku, mutumin ya nemi auranta cikin yanayi na so da kauna kuma kebance su biyu.
A cikin bidiyon mai sakan 20, matashin ya durkusa a gabanta don neman aurenta yayin da ta mika masa hannu domin karbar zoben.