Saturday, June 1, 2024

Boko Haram: An Bayyana Sunayen Manyan ‘Yan Ta’adda Da Suka Mika Kan Su Ga Sojoji A Borno

Manyan Labarai

Karamar Hukumar Gwoza, Jihar Borno – Wata kwakwarar majiya ta bayyanawa yan jarida cewa a kalla manyan kwamandojin Boko Haram hudu ne suka mika wuya ga sojojin Najeriya a jihar Borno.

The Cable ta tattaro cewa kwamandojin sun mika makamansu a ranar 12 ga watan Disamba ga dakarun sojojin Operation Hadin Kai (OPHK) da ke sintiri a karamar hukumar Gwoza a jihar ta arewa.

 

Sojojin Najeriya
Dakarun Sojojin Najeriya. Hoto: Rundunar Sojojin Najeriya

 

Sunanan kwamandojin da aka bada sune Mala’ana (Khaid), Abu Dauda (Munzir), Modu Yalee, da Bin Diska, (Nakif).

Boko Haram/ISWAP: Yan ta’adda 10 sun mika makamansu a Borno

A kalla wasu da ake zargin yan ta’addan Boko Haram/ISWAP da yaransu ne suka mika wuya ga dakarun sojojin `151 da ke jihar Borno.

Maza manya 10 da yara 5 sun mika kansu a ranar Lahadi, 3 ga watan Afirilu, a Banki, karamar hukumar Bama, Zagazola Makama, kwararre majiyar bayannan sirri ya bayyana.

An tattaro cewa yan ta’addan da suka mika wuya yan bangaren Boko Haram ta JAS, karkashin jagorancin Malam Bakura Salaba, Sahara Reporters ta rahoto.

Makama, babban mai nazarin harkokin tsaro da yaki da ta’addanci a Tafkin Chadi, ya bayyana cewa sun ajiye makamansu ne saboda luguden wuta da hare-hare da sojojin Operation Hadin Kai ke musu.

Tushe: News Brief Hausa

Duba nan: