Thursday, May 30, 2024

Bidiyon Kyayyawar Budurwa Sanye Da Atampa Tana Buga Kwallon Kafa Cike Da Kwarewa Ya Yadu

Manyan Labarai

Wata kyakkyawar budurwa wacce ke da kwarewa sosai a harkar kwallon kafa ta baje iyawarta a wani bidiyo da ya yadu a dandalin TikTok

Bidiyon wanda shafin Aboubakar Siddiki ya wallafa ya nuno yadda matashiyar budurwa ke taka leda cike da kwarewa

Ta rike tamolar sannan ta dungi jefa shi da kafa na tsawon lokaci kafin ya sauka daga kafar tata kuma ya ja hankalin jama’a

Wata kyakkyawar budurwa ta dauka hankalin jama’a a duniyar yanar gizo bayan ta nuna kwarewarta a harkar kwallon kafa a wani bidiyon TikTok.

Shafin wani mai suna Aboubakar Siddiki ne ya wallafa bidiyon mai ban sha’awa a manhajar TikTok.

Abun da ya fi ba da mamaki, budurwar na sanye ne da atampa dinkin riga da zani amma hakan bai hana ta iya buga kwallon cike da kwarewa ba.

Ta dauki kwallon kuma daga yadda ta rike shi za ka gane karara ta kware sosai a harkar buga tamolar.

Bidiyon kyakkyawar yarinya da tamola

Budurwar ta ajiye tamolar sannan ta dauke shi da kafa inda ta fara jefa shi sama sau da dama.

Mutane da dama na ta tsammanin kwallon zai fado daga kafarta, amma ta rike shi na tsawon lokaci kafin ya kubce mata.

Kwarewarta ya haifa da martani daban-daban daga mutane inda suke tambayar dalilin da yasa bata shiga harkar taka leda ba a matsayin kwararriyar yar kwallo ba.

Kalli bidyon a nan

Jama’a sun yi martani

@Teeswagkd ya ce:

“Wani ya fada mun a ina zan same ta.”

@user3172457851487 ya ce:

“Daga wace kasa wannan yarinyar ta fito.”

@Barde151 ya yi martani:

“Ki ci gaba aikinki na kyau.”

@11111 ya yi martani:

“Nuna masu yadda yan Fulani ke da hazaka.”

@chukwunnaemeka365 ya ce:

“Gaskiya tana da hazaka.”

@user Fatimah ta yi martani:

“Tana bukatar tallafi, ina kaunarki yarinya.”

@sulaimanharuna416 ya ce:

“Kina da kokari.” 

@chikekevin ya ce:

“Yanzu na gwada, daya na iya yi.”

@chukwunnaemeka365 ya ce:

“Nima ina da daya yar karama a nan.”

@Abdul Ice:

“A cikinmu, kusan 90% ba za su iya wannan ba.” 

A gefe daya, wani manomi dan kasar Uganda, Musa Hasahya wanda ke da mata 12 da yaya 102 – tare da jikoki 568 – daga karshe ya yanke shawarar dena haihuwan yara baki daya.

Musa Hasahya, dan shekara 67, yanzu ya umurci matansa su fara kayyade iyalai, don su iya samun kudin siyan abinci da kula da iyalansa masu yawa.

Duba nan: