Wednesday, May 29, 2024

Ba Zan Yi Soyayya da Wanda Ba Zamu Rika Jin Dadin Juna Ba, Jaruma

Manyan Labarai

Shahararriyar jaruma ta shirin fina-finan Najeriya ta bayyana ra’ayinta game da wani batu da ake tattauna wa a kafafen sada zumunta wanda ya shafi soyayya.

Jaruma a masana’antar shirya-shirya fina-finan Nollywood da ke kudancin Najeriya, Nkechi Blessing, wacce ta yi fice tace ba zata yi soyayya da mutumin da bai waye ba ta bangaren amfani da albarkatun jikin mace.

Jarumar ta bayyana haka yayin da take fadar ra’ayinta kan batun soyayya babu jin dadin juna da ake tattauna wa a soshiyal midiya.

A cewar kyakkywar jarumar, ba zata shiga layin kalar wannan soyayyar ba wacce namiji ba zai rika kwanciya da ita suna sharholiyarsu ba, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Jarumar ta kafa hujja kan matsayarta da cewa idan mutum zai sayi mota ya kan hau ya ɗana domin sanin karfin injin da nagartarsa haka zalika idan zaka sayi Naman suya, masu sana’ar su kan ba mutum dandano kafin ya siya.

Nkechi Blessing ta bayyana cewa jima’i ko da babu aure abu ne mai matukar dadi kuma ita kam ba zata rayuwa wurin da babu wannan sharholiya ba.

A kalamanta tace:

“Nan ba inuwar kowa bace, mutane na sayen motoci su shiga su dana don duba lafiyar Inji. Haka nan idan zaka sayi naman suya, za’a baka dandado kafin a yanka maka na daidai kuɗinka.”

“Ba dai ni ba kam, abun nan fa akwai dadi, gaskiya ba zan zauna a irin wannam soyayyar ba ko kadan.”

A wani labarin kuma Jaririn Da Ya Fara Zuwa Duniya a 2023 Ya Samu Kyauta Mai Tsoka Daga Matar Gwamna

Uwar gidan gwamnan jihar Ekiti, Dakta Olayemi Abiodun Oyebanji, ta gabatar da kyautar tsabar kuɗi da wasu kyaututtuka ga jaririn farko da aka haifa a 2023.

Jaririn na farko ya faɗo duniya ne da misalin karfe 12:00 na farkon ranar 1 ga watan Janairu, 2023 a Comprehensive Health Centre da ke Oke-Yadi, a Ise-Ekiti.

Duba nan: