Za a kulla auren zumunci tsakanin masarautar Kano da masarautar Bichi wadanda dukkansu tsatso ne na marigayi mai martaba sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero.
Hadadden saurayi Yarima Sanusi Aminu Bayero, zai angwance da kyakkyawar amaryarsa mai suna Gimbiya Ummi Nasir Bayero.
Yarima Sanusi ‘da ne a wurin sarkin Kano Mai Martaba Alhaji Aminu Ado Bayero yayin da ita kuma amarya Ummi diya ce a gurin mai martaba sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero.
Shafin @weddingcruize ne ya wallafa labarin a Instagram inda ya jaddada lallai aure ne za a kulla na jinin sarauta da sarauta.
Kamar yadda shafin ya wallafa, ya ce: “Wani auren na jinin sarauta, kuma dan yaya da kani ne auren. Yarima Sanusi Ado zai auri Ummi Nasir Ado Bayero. Mun ‘kagu.”
An Bankado Wasikar Soyayya Da Wata Budurwa Ta Aikewa Dan SS1, Jama’a Sun Yi Cece-kuce
A wani labarin kuma, mun ji cewa wasu amfani da soshiyal midiya sun yi martani ga wasikar soyayya da wata yarinya ta rubutawa matashi dan aji hudu a Sakandare mai suna Somto.
Yayar yaron ta wallafa wasikar a TikTok yayin da take ja masa kunne kan harkokin makarantarsa.
Ta bukaci kanin nata ya durkusa yayin da take masa tambayoyi kan siffar marubuciyar wasikar mai suna Precious.
Budurwar ta ce bata yi soyayya da kowa ba lokacin da take SS1. Kanin nata na ta dariya yayin da yake sifanta budurwa tasa wacce ta rubuto masa wasikar.
Ya bayyana cewa sun shafe tsawon watanni shida suna soyayya.
Precious ta bashi hakuri a kan rashin sumbatarsa, tana mai cewa ta yi hakan ne saboda basu dade da fara soyayya ba.
Ta kara da cewar ba za ta iya sumbatarsa a harabar gidansu ba. Precious ta yi bayanin yadda take kewar Somto sannan ta shawarce shi da ya mallaki waya don taimakawa soyayyarsu.
Budurwar ta bayyana shirinta na son aurensa sannan ta bukace shi da ya yaga wasikar bayan ya gama karantawa.